Wasu ‘yan bindiga sun hallaka ‘yan sanda biyu yayin da wasu daban biyu suka ji munanan raunuka bayan da suka kai hari a tashar bincike ta kauyen Goudel Gorou Bongo Banda da ke gab da mashigar birnin Yamai kan hanyar Ouallam.
Wannan na faruwa ne a wani lokacin da ake shirye-shiryen taron shuwagabanin kasashen Afirka da kasar ta Nijar za ta karbi bakuncinsa a farkon watan gobe.
Wakilin Muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma ya ruwaito cewa maharan wadanda ba a bayyana yawansu ba sun yi nasarar isa tashar bincike ta kauyen Goudel Gorou ne a kafa da misalin karfe 11 na dare lamarin da ya ba su damar shammatar jami’an tsaro suka bude masu wuta.
Masu nazari akan al’amuran tsaro na kallon wannan hari a matsayin wani abin da aka kitsa da gamin bakin wasu mutanen gari.
Tuni aka jibge karin jami’an tsaro a wannan tashar bincike da kewayenta yayin da ‘yan sanda suka killace wurin da abin ya faru a wani yunkurin harhada bayanan farko na binciken da zai ba da damar tantance zahirin abin da ya wakana.
Tun a farkon watan nan, gwamnatin Nijar ta sanar cewa akwai yiyuwar ‘yan ta’adda za su kwatanta kai hari a birnin Yamai mafarin abin da ya sa jami’an tsaro suka kaddamar da wani binciken ababen hawa.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:
Facebook Forum