Gwamanatin Jamhuriyar Nijar ta shigar da karar shugaban jam’iyyar Moden Lumana, Hama Amadou a gaban kotu saboda zarginsa da yunkurin katsewa jami’an tsaro hanzari a yakin da kasar ke yi da ‘yan ta’adda.
Wannan ya biyo bayan wasu kalaman da ya furta ne a wani fayfan bidiyon da ya bayyana a kafafen sada zumunta a washegarin harin da ya hallaka sojojin kasar kimanin 29.
Sai dai makusantansa na cewa bita da kullin siyasa ne kawai.
Fayfan bidiyon wanda hukumomin Nijar suka haramta wallafa shi ta kowace irin kafa na dauke ne da wani sako wanda a cikinsa Hama Amadou ke nuna jin takaici akan abin da ya kira gazawar gwamnatin Nijar wajen shayo kan matsalar tsaro.
Ya kara da cewa gwamnatin na amfani da yanayin tabarbarewar tsaron da ake ciki don aika wani rukunin sojojin kasar lahira dagangan yayin da wasu akan korer su gaba daya daga bakin aikin soja akan dalilan da ba su da mahimmanci.
Tuni dai ma’aikatar tsaro ta kasa ta ba da sanarwar kan wannan magana a gaban kotu akan bukatar ta yi hukunci kamar yadda ministan tsaro Alhaji Kalla Moutari ya tabbatar.
Ana su bangare magoya bayan jam’iyar Moden Lumana irinsu Bana Ibrahim na kallon matakin na gwamnatin Nijer a matsayin wani bita da kullin siyasa.
A cikin wannan sakon bidiyo jagoran na ‘yan adawa ya kuma zargi mahukuntan Nijar da rashin bai wa dakarun kasar wadatattun kayan yaki lamarin da yake ganin shi ne ke kawo cikas a wannan yaki da ya ki ci ya ki cinyewa.
Sai dai su ma hukumomi sun musanta wannan zargi.
Saurari cikakken rahoton Sule Mumuni Barma daga Yamai.
Facebook Forum