A yayin da jamhuriyar Nijer ke ci gaba da zaman makokin sojojinta kusan 30 da ‘yan bindiga suka hallaka a yammacin ranar Talatar da ta gabata a kusa da garin Tongo Tongo, shugaba Issouhou Mahamadou ya jaddada aniyar ci gaba da jajircewa domin murkushe kungiyoyin ta’addanci a yankin tafkin Chadi da yankin Sahel kamar yadda aka fatattake su a Iraki da Syria.
A wunin farko na zaman makokin kwanaki uku da aka shiga a baki dayan kasar ta Nijer ne shugaba Issouhou Mahamadou ya ziyarci sojojin dake kwance a asibitin Hospital De Reference domin duba halin da suke ciki sanadiyar harin ta’addancin da ya hallaka abokan aikinsu guda 28 a kauyen Balley Beri, kusa da Tongo Tongo dake kan iyakar Nijer da Mali.
Shugaban kasar ta Nijer ya sake isar da gaisuwar ta’aziya zuwa ga iyalan wadanda suka rasu tare da fatan Allah ya yi masu Rahama albarkacin watan nan na Ramadan, wadanda suka jikkata kuma da fatan Allah ya koro masu sauki.
Shugaba Issouhou Mahamadou, ya jaddada aniyar ci gaba da daukar matakan tabbatar da tsaron jama’a da dukiyoyinsu tare da dagewa kai da fata domin kare iyakokin Nijer.
Ya ce yayi imani ko-ba-jima ko-ba-dade in Allah ya yarda za su ga karshen wadannan miyagun kungiyoyin dake haddasa asarar rayuka kamar yadda aka gama da su a Iraki da Syria.
Reshen kungiyar IS a yankin sahara ne ya dauki alhakin kai wannan mummunan harin dake ci gaba da daurewa jama’a kai.
A wunin yau Jumma’a ministan tsaron kasar Nijer, Kalla Moutari da babban kwamandan rundunar mayakan tsaron kasar da makarabansa suka zagaya gidajen sojojin da suka kwanta dama domin jajanta masu, a yayinda aka umurci gwamnonin jihohi su ma su je gidajen sojojin da harin ya rutsa da su domin jajanta masu.
Ga karin bayani cikin sauti daga Souley Mummuni Barma.
Facebook Forum