A Jamhuriyar Nijar an shiga zaman dar-dar a birnin Maradi, sakamakon wata zanga zangar da ta barke a jiya da daddare, kuma aka wayi gari da ita.
Boren ya faru ne bayan da hukumomi suka cafke wani limamin masallacin juma'a da ake zargi da yunkurin tunzura jama'a su bijirewa wata dokar da gwamnatin kasar take shirin samarwa, wacce ta gabatarwa a majalisar dokokin kasar.
A birnin Yamai kuma kungiyoyin addinin Islama na ci gaba da kiraye-kirayen kwantar da hankali.
Matakin cafke limamin masallacin juma’a na Sahaba da ke unguwar Zaryar birnin Maradi, shi ne ya harzuka matasa suka fito kan tituna suna cinnawa tayoyi wuta.
Ainihin dokar da ke ba da izinin sanya ido akan batutuwan da suka shafi gina wuraren ibada da ma yadda ake tafiyar da su wacce gwamnati ta aikewa majalisar dokoki, ita ce ta haddasa rudani a kawunan al’umma, dalili kenan da ya sa dan majalisa mai wakiltar al’ummar jihar Maradi Alh. Sani Atiya ke jan hankula da a zauna lafiya.
A Yamai wasu kungiyoyin addinin Islama kimanin 8 a karshen wani taron wa’azi da ya gudana a jiya Asabar da daddare, sun gargadi majalisar dokokin kasa da ta yi watsi da wannan kudirin doka yayin da suka yi kiran jama’a akan batun zaman lafiya.
A farkon makon gobe ne majalisar dokokin kasa ke sa ran nazari akan kudirin dokar saka tsari a sha’anin gudanar da wuraren ibada da makarantun allo, da nufin kaucewa rigingimu masu nasaba da dalilan addini, matakin da ya samo asali daga shawarwari, a karshen taron da ya hada malaman musulunci da hukumomi a Yamai a watan Nuwamba shekarar 2017.
Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum