Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Kudiri Aniyar Kafa Dokar Amfani Da Yanar Gizo


Tamburan kafafen sada zumunta
Tamburan kafafen sada zumunta

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kudiri aniyar tsaurara matakan yaki da masu amfani da yanar gizo wajen cin zarafin jama’a ko wadanda ke aikata ayyukan asha a wannan lokaci da bayanai ke nuni da cewa kungiyoyin 'yan ta’adda na amfani da wannan hanya wajen yada farfagandar neman magoya baya.

Lura da yadda masu amfani da yanar gizo ta mahimmiyar hanya ke kara bijiro da sabbin dubaru domin tafka ta’asa akan harkokin jama’a ya sa gwamnatin Nijar yanke shawarar kara tsaurara matakai.

Hakan a cewar hukumomi, hanya ce ta tunkarar wannan babban kalubale da ke barazana ga zaman lafiya kamar yadda wata sanarwar da aka bayar a karshen taron Majalisar Ministoci masu kare hakkin dan adam.

Sanya ido akan irin ayyukan da ke gudana a yanar gizo da tsaurara hukunci akan wadanda aka kama da laifin aikata abubuwan da suka sabawa doka na daga cikin mahimman matakan da ke kunshe a wannan kudirin doka.

Anan gaba ne gwabnatin Nijar za ta gabatar da wannan kudirin doka a gaban Majalisar Dokokin kasa domin nazari akansa kafin ta yi na’am da abubuwan da ya kunsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG