A jamhuriyar Nijar mabiya mazhabar shi’ah sun yi jerin gwano a birnin Yamai, a yau juma’ar karshen watan Ramadan, da nufin nunawa duniya rashin jin dadinsu akan halin kuncin da Falasdinawa ke ciki, lamarin da ya sa suka kona tutar kasar Isra’ila a matsayin jan kunne ga manyan kasashe duniya.
Yau da hantsi lokacin da ‘yan shi’ah ke kan hanyar zuwa dandalin Chateau tawaye, dake unguwar lazaret a birnin Yamai, inda suka saba gudanar da taron muzahara na juma’ar karshen watan Ramadan.
Ja-yayyar da ake ci gaba da fuskanta akan batun mallakar masallacin Qudus, da kashe kashen dake tattare da wannan al’amari, na kan gaba cikin batutuwan da jagoran mabiya shi'ah Shiek Ahmed Lazaret ya tabo a jawabinsa.
Matasa wadanda ke kallon wannan rana ta juma’ar tunawa da al’umar Falasdinu da muhimmanci, sun jaddada aniyar ci gaba da fafutikar ganin masallacin Qudus ya koma hannun su inji Dahirou Moussa da ake kira Chadoua.
Lura da yadda jinsin mata ke dandana kuda a rikicin Isra’ila da Falastinawa ya sa mata ‘yan shi’ah sadaukar da komai nasu don ceton takwarorinsu daga wannan tashin hankali.
Malama Sa’adatou Aboubakar, na daga cikin masu irin wannan tunani a taron muzaharar wannan shekara, ta kona tutar Isara’ila a matsayin hannun ka mai sanda ga kasashen yammaci, saboda irin gudunmawar da suke badawa wajen ruruta wutar.
Ga rahoton wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum