A jamhuriyar Nijar yau aka yi bikin damka wa hukumomin tsaron kasar wani tallafin kayayakin soji, wadanda aka kiyasta darajarsu kudin su kimanin dolla Amurka miliyan 21, domin rundunar hadin gwiwar G5 Sahel mai yaki da ‘yan ta’adda a kasashe 5 na yankin sahel.
Tallafin wanda ke kunshe da wasu sabbin motoci da wasu mahimman kayayakin sadarwa, gudunmawar da kasar Amurka ta yi alkawalin bayar wa, da nufin karfafa gwiwa ga rundunar G5 sahel a yakin da dakarunta ke karawa da ‘yan ta’adda inji jakadan Amurka a Nijar Amb. Eric P. Whitaker, lokacin da yake damkawa hukumomin tsaro makullan wadannan motocin.
Jami’in hulda da ‘yan jarida a ofishin jakadancin Amurka a Nijar Alhaji Idi Bara'u shine yayi mana karin bayani.
Ministan tsaron kasar Nijar Alhaji Kalla Moutari, dake karbar wannan tallafi ya jinjinawa gwamnatin Amurka, saboda a cewarsa ta yi tsayin daka akan maganar samarda tsaro a yankin sahel. Ya nuna cewa wadanan kayayyaki zasu yi amfani sosai wajen murkushe ‘yan ta’addan kan iyakokin Nijar, Mali da Burkina Faso.
Wannan tallafi ya zo ne bayan kwana biyu da shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou ya gana da jakadun Amurka da Faransa a fadarsa, haduwar da ta kasance suka samu damar tantaunawa a tsakanin hafsoshin sojan kasashen 3, inda suka bullo da wasu sabbin dubarun yaki da ‘yan ta’adda.
A jajibirin karamar Sallah hukumomin Nijar sun sanar da cewa sojojin kasar sun karkashe ‘yan boko haram sama da 50 a yankin Diffa, yayinda aka kama wasu 2 dauke da bom da suke shirin tayarwa bayan wadanda dubunsu ta cika anan Yamai, su ma a wani lokacin da suke shirin kai farmaki.
A saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum