Ofishin jakadancin Amurka a jamhuriyar Nijar ya shirya liyafar bude baki ma Musulmin kasar, albarkacin watan Ramadan abinda ya sami yabo daga shuwagabanin kungiyoyin ci gaban al’uma, a bisa la’akari da yadda zai kara karfafa zumunci a tsakanin mabiya addinai mabambanta.
Al’ada ce a kowace shekara idan irin wannan lokaci na azumin Ramadan ya zagayo ofishin jakadancin Amurka a Nijar kan gayyaci Musulmin kasar a babbar liyafar da ake shiryawa takanas domin bude baki, abinda ke zama wata hanyar kara tunatarwa akan mahimmancin mutunta abokan zama ba tare da la’akari da wani bambancin addini ba…
Jakadan Amurka a Nijar Ambasada. Eric P. Whitaker ya bayyana cewa sanin kowa ne Musulunci addini ne da ke bukatar mutane su kusanci juna, su kasance masu zaman lafiya da taimakon juna, musamman a lokacin Ramadan. Sau dari na sha ganin irin wannan halayya ta na faruwa a tsakanin ‘yan Nijer da baki mazauna wannan kasa, kamar yadda a yanzu haka dubban mutanen da suka gudo daga kasashensu sanadiyyar tashe-tashen hankula ke samun mafaka.
Kusan dukkan wasu shuwagabanin kungiyoyin ci gaban al’uma sun halarci wannan liyafa ta bude bakin azumin Ramadan, cikinsu har da shugaban kungiyar makiyayan arewacin Tilabery Bubakar Diallo.
Haka su ma kungiyoyin mata sun amsa gayyatar ta ofishin jakadancin Amurka a Nijar. Hajiya Rabi Djibo Magaji ita ce shugabar kungiyar samar da zaman lafiya, APAISE.
A karshen wannan haduwa hadakar kungiyar mata, shuwagabanin kamfanoni da masana’antu masu zaman kansu, ta karrama jakadan Amurka, Ambasada Eric P. Whitaker da shugabar cibiyar raya al’adun Amurka a Nijar, Cynthia Faby, da lambobin yabo saboda abinda aka kira tallafin da su ke bayarwa domin ci gaban kananan kamfanoni da masana’antun cikin gida.
Ga cikakken rahoton daga Souley Moumouni Barma:
Facebook Forum