Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutuwar Mutane Sama Da Hamsin: An Fara Zaman Makoki A Jamhuriyar Nijar


Tankar Mai
Tankar Mai

A jamhuriyar Nijer yau aka fara Zaman makoki na kwanaki uku da nufin nuna alhinin rasuwar mutane sama da hamsin, da suka Kone kurmus.

A jamhuriyar Nijar yau aka fara Zaman makoki na kwanaki uku da nufin nuna alhinin rasuwar mutane sama da hamsin, da suka Kone kurmus a yayinda wata motar dakon mai ta kama da wuta jim kadan bayan faduwarta a mashigar birnin Yamai da daren Lahadi, wayewar Litinin da ta gabata.

Wakilinmu na Muryar Amurka ya aiko mana karin bayani, cewa a karshen taron Majalisar Tsaro ta Kasa wanda ya gudana da yammacin jiya Talata a karkashin jagorancin Shugaba Mahammamdou Issoufou a fadarsa ne hukumomin jamhuriyar Nijar suka bada sanarwar soma zaman makoki na tsawon kwanaki uku; daga yau Laraba domin nuna juyayin rasuwar mutanen nan kimanin hamsin da biyar da suka kone kurmus. Elhadji Ider Adamou shine magatakardan ofishin ministan cikin gida.

Kokarin jin ta bakin dangin wasu daga cikin wadanda abin ya shafa ya citura sakamakon yanayin alhinin da suke ciki, to amma wasu mazaunan Yamai da aka tuntuba kan wannan batu sun bayyana cewa shuwagabaninn addinai, irinsu Ustaz Moha Halil mamba a kungiyar addinin Islama ta AIN, na jan hankulan jama’a akan mahimmancin irin wannan lokaci na zaman makoki.

Da yammacin shekaran jiya Litini ne aka yi jana'izar wadannan mamata, wasu kuma sama da talatin ne ke kwance a asibitoci daban-daban na birnin Yamai, yayinda dreban tankar da ta yi wannan hatsari ke tsare a hannun jami'an tsaro, matakin da ake dangantawa da dalilan bincike.

Ga cikakken rahoton daga wakilinmu Sule Mummuni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG