A wani yunkurin dakile hanyoyin da kungiyoyin ta’addanci ke amfani da su don neman hadin kan jama’a a aika-aikar da suka sa gaba, gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kudiri aniyar tsaurara matakan saka ido akan batutuwan da suka shafi sha’anin ibada.
Gwamnatin ta dauki matakin ne don ganin cewa mabiya addinai mabambanta sun ci gaba da mutunta juna.
Taron majalisar ministoci na baya-bayan nan ne ya ba da sanarwar bullo da wannan mataki da ke matsayin na rigakafin kaucewa faruwar fitintinu masu nasaba da dalilan addini da aka saba gani a kasashe da dama musamman inda kungiyoyin ta’addanci ke cin karensu ba babbaka.
Halin da ake ciki a yau, a Nijar da makwabta ya kai matsayin da za a zuba ido sosai akan sha’anin gudanar da addinai, mafarin da gwamnatin wannan kasa ta kudiri aniyar daidaita sahu.
"Yau za iske ana gina masallatai a bakin hanyoyi, ba a san su ya gina su ba, mutum in zai yi masallaci ya nemi iznini." Inji Dr. Hassan Malan Gamkalle wani masanin shari’ar musulunci ne.
Shuwagabanin addinin kirista ana su bangare ma sun yi na’am da wannan mataki da suke ganin ya zo akan lokaci inji mataimakin shugaban kungiyar majam’iun Nijar (AMEN,) Pastor Hasan Dan karami.
A watannin da suka gabata, rahotani daga yankin Tilabery sun yi nuni da cewa kungiyoyin ta’addanci na shirya wa’azin cusawa jama’a tsattsauran ra’ayi a kauyukan da suka kai farmaki wadanda ke kan iyakar Nijar da Mali, lamarin da ya sa hukumomi tsaurara matakan tsaro.
A nan gaba kadan ne gwamnatin ta Nijar za ta gabatar wa majalisar dokokin kasa wannan kudirin doka da nufin neman hadin kanta game da maganar zuba ido a kan sha’anin gudanar da ibada.
Saurari rahoton Sule Mumuni Barma domin karin bayani:
Facebook Forum