Lamarin tsaro na ci gaba da sake tabarbarewa a karamar hukumar Barikin Ladi dake jihar Filato, rikicin da ya samo asali tsakanin al’umomin Fulani da Birom.
Jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar da babban taronta a Dandalin Eagle dake babban birnin Abuja.
Al’umomin Fulani da na Birom dake karamar humar Barikin Ladi a jihar Filato, sun bukaci hukumomin tsaro da su dukufa wajen gudanar da aikinsu na tsaron lafiyar jama’a da dukiyoyinsu.
A yau ne taron kasa da kasa na hafsohin hukumomin leken asiri na rundunonin kasashen yankin tafkin Chadi ke shiga rana ta biyu, inda babban hafsan rundunar sojojin Najeriya ya dauki lokaci mai tsawo yana jawabi kan ta’addancin Boko Haram.
Ciki da Gaskiya Wuka Bata Hudashi
Ministan babban birnin Tarayya Abuja Muhammad Musa Bello ya kafa dokar takaita zirga zirga a garin Bwari da ta fara aiki yau daga misalin karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe.
Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya bayyana faifan bidiyon da ake yadawa a kafar sada zumunta dake nuna gwamnan yana kiran ‘yan Najeriya da su baiwa shugaba Buhari goyon baya, a matsayin tsohon bidiyo ne.
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya karfafa yakin da yake na cin hanci da rashawa ta hanyar sanar da cewa za a binciki dukkan ma’aikatan gwamnati don gano hanyoyin da suke samun kudadensu.
Bayan kammala ibadar azumin watan Ramadan miliyoyin mutane sun halarci sallar idi a ko ina a fadin Najeriya.
Babban sufeto Janal na ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya ce dole ne doka tayi aiki kan kowanne dan Najeriya komai girmansa ko mukaminsa.
Jam’iyyar Action Democratic Party (ADP) ta Najeriya ta nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnatin APC ke tafiyar sha’anin mulkin kasar.
Kwanaki hudu kenan wasu barayin shanu a jihar Zamfara ke addabar wasu kauyuka da suka kai goma, wanda hakan yayi sanadiyar raba dubban mazauna kauyukan da gidajensu.
Majalisar Dokokin Najeriya ta yi gyara a sabuwar dokar zaben nan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki sa hannu a kwanakin baya.
Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta ce tana fuskantar barazana daga rundunar sojojin Najeriya bisa yadda take gudanar da aikinta na ba sani ba sabo.
Ana ci gaba da yin mahawara kan yadda hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta ke mikawa wadanda take tuhuma kwali ko allo dake rubuce da laifi maimakon tuhuma da ake musu, kuma su daga a dauki hotonsu.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ba zata mayar da wani martani ba a yanzu dangane da sharudan da Majalisar ‘kasa ta mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da mutuwar wasu ‘yan Sanda uku dake kwantar da tarzoma a wani kwantan bauna da wasu mahara suka yi musu a mararrabar Udege.
Matsalar tattalin arziki a Najeriya ya ragewa kasuwar China Town dake birnin Legas armashi.
Domin Kari