Kakakin ministan Abuja Mallam Abubakar Sani, ya shaidawa sashen Hausa na Muryar Amurka cewa daukar wannan mataki ya biyo bayan yinkurin tayar da wani mummunan hargitsi da wasu bata gari suka so suyi a dai dai lokacin da Mai Martaba Sarkin Bwari ke hawan Sallah.
Ministan na Abuja ya fada cikin wata takardar sanarwa da kakakinsa Alhaji Abubakar Sani ya fitar cewa, dokar zata ci gaba har sai al'amuran tsaro sun daidaita a yankin. A shekarar da ta gabata lokacin bikin kirsimeti, aka kone babbar kasuwar garin kurmus baya ga asarar rayuka.
Burbushin wancan rikicin ne kuma ya sake kunno kai a wannan lokaci, wanda ba dan matakan gaggawa da ministan Abuja ya dauka ba da al'amura sun rikice.
Ministan na Abuja ya yi gargadin cewa gwamnatin za ta sa kafar wando daya da duk masu son kawo rikici a Bwari da ma sauran yankunan na nabban birnin tarayya.
Mai Sharhi kan al'amuran birnin tarayyar Najeriya, Sani Gamco ya koka bisa yadda wannan rikici na Bwari yaki ci yaki cinyewa, yana mai dora musabbabin abin kan Rikicin sarauta tsakanin manyan kabilu biyu na garin wato Koro da Gbagyi.
Sani Gamco ya ce muddin ba a samo bakin zaren ba, to kuwa za a ci gaba da ganin irin wannan fitina da baza ta haifarwa kowa da mai ido ba. Don haka yayi fatan ministan na Abuja zai dau matakan kawo karshen fitinar baki daya.
Wakilin Muryar Amurka Hassan Maina kaina wanda ya ziyarci garin ya fahimci hankali ya kwanta jama'a na ci gaba da hada-hada duk kuwa da zaman dar dar a yankin, yayin da jami'an tsaro ke ta yin sintiri cikin shirin ko ta kwana.
A fadar Sarkin Bwari, ana ci gaba da bukukuwan wasan Sallah cikin tsauraran matakan tsaro.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum