Jam’iyyar ADP ta gudanar da wani taro a birnin Minna jihar Neja, na murnar cika shekara daya da kafa ta, jam’iyyar ta ce ta damu matuka da yadda gwamnatin APC ta kasa shawo kan kisan jama’a a jihar Zamfara da kuma birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Dakta Haruna Usman Dangajere, dake zama mataimakin sakatare na jam’iyyar a Najeriya, ya ce abin da ke faruwa a jihar Zamfara da birnin Gwari abune mai ban mamaki, ganin yadda aka fara da kashe mutum daya mutum biyu, sai gashi yau an wayi gari ana kashe mutum sama da dari.
Shugaban jam’iyyar ADP a jihar Neja, Tanimu Sarki Kwamba, yace suna cikin wani yanayi na farin ciki akan cika shekara daya da kafa jam’iyyar, haka kuma sun shiryawa zabe mai zuwa.
Tanimu Sarki, ya ce ganin yadda jihar Neja ke samun kudade amma babu wani aiki da ake gudanarwa a jihar.
Da yake mayar da martani gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya ce duk wata matsala da suke fuskanta a yanzu sun gajeta ne daga gwamnatocin baya.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum