Rahotanni na nuna da cewa an kashe ‘Yan Sandan ne kan hanyarsu ta zuwa kwantar da rikici da ya barke tsakanin kabilar Agatu da Fulani, yayin da aka afka musu aka kashe su.
Kakakin rundunar ‘Yan Sandan jihar Nasarawa Isma’il Usman, ya fadawa Muryar Amurka cewa yanzu haka zaman lafiya ya dawo yankin bayan da aka aika da jami’an ‘Yan Sanda, kuma ana ci gaba da kokarin an kamo duk wadanda ke da hannu a kisan.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah a jihar Nasarawa Muhammad Usaini, yayi tir da faruwar lamarin tare da bayar da shawarar a gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata kisan.
Tun farko dai wasu rahotanni sunce maharan sun kashe mutane takwas, suka kuma cinnawa gidaje masu yawa wuta a kauyukan Agatu.
Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Almakura, ya ce gwamnati na daukar matakan tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Zainab Babaji.
Facebook Forum