Masana harkokin tsaro a Najeriya na ganin ‘karin daukar jami’an ‘Yan Sanda aiki shine masalahar tsaro a kasar.
Rundunar ‘Yan Sandan Najeirya ta gayyaci shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki domin amsa tambayoyi, kan alakarsa da ‘yan fashin da suka kai hari garin Offa na jihar Kwara.
Babban hafsan hafsoshin rundunar sojojin ruwan Najeriya ya yi tsokaci kan atisayen da rundunar sojojin ruwan Amurka ta jagoranta na sama da kasashe 30 a gabar tekun Guinea, don karfafa tsaro a yankin.
Kungiyar al’ummar Berom dake fadin Jihar Filato ta yi kira ga gwamnatocin tarayya da ta jiha, da su dauki matakan gaggawa wajen dakatar da kashe-kashen da ake yiwa jama’a a wasu sassan jihar.
Sha’anin ayyukan kwamitocin ‘yan Majalisun Dokokin Najeriya ya shiga cikin jerin batutuwa dake janyo cece-kuce a tafiyar siyasar kasar.
Dan Majalisar Wakilai dake wakiltar mazabar Kachia da Kagarko, Adams Jagaba, ya sauya sheka daga jam’iyya mai mulki zuwa jam’iyyar adamawa ta PDP.
Babbar kotun birnin tarayya ta yanke hukuncin daurin shekaru 14 ba tare da zabin biyan tara ba ga tsohon gwamnan jihar Taraba Reverend Jolly Nyame
Matasa a Najeriya sun fara bayyana farin ciki dangane da alkawarin shugaba Muhammadu Buhari na sanya hannu akan dokar rage shekarun tsayawa takarar zabe a kasar domin baiwa matasan damar shiga a dama dasu a fagen siyasar kasar.
Ciki da Gaskiya Wuka Bata Hudashi
‘Yan Najeriya mazauna Jamhuriyar Nijar sun gudanar da zaben mutanen da za su jagoranci kungiyarsu a ci gaba da kara inganta matakan samar da hadin kai tsakanin ‘yan kasar a duk inda suke.
Amfani da miyagun kwayoyi na kawo rarrabuwan kawuna tsakanin iyali, inda wasu lokutan ta kan kai ga kisa ko yiwa iyaye rauni.
Bayan lokaci mai tsawo da ta dauka tana mahawara akan amincewa da dokar kafa kungiyar zaman lafiya ta Peace Corps, Majalisar Wakilan Najeriya ta yi fatali da dokar gaba daya.
Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF yayi gargadin cewa barkewar cutar Ebola a jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na barazana ga lafiya da walwalar yara, haka kuma dole ne a dauki matakai na musamman don taimakawa rayuwar yaran.
Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyarar aiki birnin Kano, inda ya tabbatar da shirin gwamnatin tarayya na tallafawa 'yan kasuwa da kananan masana'antu.
Kasashen Netherlands da Australia sun ce Rasha suke dorawa laifi kuma zasu nemi diyya akan fadowar jirgin saman nan na Malaysia mai lamba MH17 da ya fado a yankin gabascin Ukraine da ake yaki a cikinsa shekaru hudu da suka gabata, har dukkan mutane 298 da ma’aikatan jirgin suka hallaka.
Kasar Korea ta Arewa a ta ce har yanzu a shirye take don zaman tattaunawa da Kasar Amurka a kowanne lokaci a kuma duk irin yanayin da take bukata, biyo bayan soke ganawar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un.
Wasu mutane biyu dake dauke da cutar Ebola sun gudu daga asibitin da aka killace su a Kasar Jamhuriyyar Demokradiyar Congo don halartar wani taron addu’a, ana fargabar cewa mai yiyuwa sun harbi akalla mutane hamsin da suka yi cudanya da su a wurin taron.
Mu’amula tsakanin tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da shugaba Muhammadu Buhari ta shiga wani hali.
Domin Kari