Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Taron Shugabanin Hukumomin Leken Asirin Kasashen Yankin Tafkin Chadi a Abuja


ABUJA: Manyan Janar Janar na leken asirin rundunar sojin Najeriya
ABUJA: Manyan Janar Janar na leken asirin rundunar sojin Najeriya

A yau ne taron kasa da kasa na hafsohin hukumomin leken asiri na rundunonin kasashen yankin tafkin Chadi ke shiga rana ta biyu, inda babban hafsan rundunar sojojin Najeriya ya dauki lokaci mai tsawo yana jawabi kan ta’addancin Boko Haram.

Baban hafsan hafsoshin rundunar sojojin Najeriya janar Abayomi ya yi bayani a taron manyan hafsoshin leken asiri na rundunonin kasashemn yankin tafkin chadi da akeyi da hadin gwiwa da rundunar sojin Amurka da ke Afrika da ake kira AFRICOM dake gudana a Abuja.

Ya ce rawar da bayanan sirri zai taka na samar da zaman lafiya a yankin tafkin chadi ba zai misaltu ba don haka akwai bukatar musayar bayannan sirri da aiki tare tsakanin kasashe, shiyoyi da ma nahiyoyi daban daban don hakka ta cimma ruwa, a don haka ya ce yana da yakinin wadannan masu halartar wannan taron a halin yanzu zasu lalubo hanyar samar da kwanciyar hankali a yankin na tafkin chadi.

Kazalika ya bada missali ga yadda suka tunkari ‘yan ta’addar Boko Haram inda ya ce sun samu nasarar yakar masu tsatsauran ra’ayi bayan da suka yi wa rundunar sojojin su garanbawul da hakan ya sa suka matsa kaimi wajen yakar Boko Haram.

Rundunar dakarun kasashen tafkin chadi, na gudanar da aikin Operation amnufakat yayin da a Najeriya ta kaddamar da atisayen last call duk daI a kokarin ta na kawo karshen mayakan boko haram.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG