Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Jihar Gombe Na Da Damar Tsayawa Takarar Duk Mukamin Da Suke So - Dankwambo


Gombe
Gombe

Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya bayyana faifan bidiyon da ake yadawa a kafar sada zumunta dake nuna gwamnan yana kiran ‘yan Najeriya da su baiwa shugaba Buhari goyon baya, a matsayin tsohon bidiyo ne.

A shafinsa na Twitter gwamnan ya bayyana faifan bidiyon a matsayin tsohon ‘dauka ne da aka yi tun ranar bikin dimokaradiyya na shekara ta 2015.

Da yake jawabin karamar sallah gwamnan ya bayyana cewa ‘yan jihar Gombe suna da damar neman duk wani mukami kowanne iri ne.

Irin furucin da gwamna Ibrahim Dankwambo ya yin a nuni da cewa zai shiga takarar shugabancin kujerar Najeriya a shekarar 2019.

A halin da ake ciki kuma, ruwa da iska mai karfin gaske yayi sanadiyar asarar rayuka da rugujewar gidaje, a dukkan yankunan kananan hukumomin jihar Bauchi.

Har ya zuwa yanzu dai babu wata kididdiga a aka fitar a hukance yawan asarar da ta faru.

Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG