Majalisar dai ta mika wasu bukatu guda 12 ga shugaba Muhammadu Buhari, bayan da Majalisar ta yi wani zama akansu kuma take bukakatar shugaban ya aiwatar da su ko kuma su saka kafar wando daya.
Kakakin fadar shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu, tun farko ya bayyana cewa ba zasu yi wata magana akan batun ba tukunna, sai dai wata kila a nan gaba. Amma jam’iyyar APC ta fito fili ta bayyana cewa tana daukar mataki na kawo sulhu tsakanin bangarorin guda biyu.
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen arewa maso yammacin Najeriya, Inuwa Abdulkadir, ya fadawa Muryar Amurka cewa a jam’iyyance jam’iyya ta siyasa itace uwa, itace uba ga duk wani dan takara, saboda haka dole ne jam’iyyar ta dauki mataki don tabbatar da cewa an sasanta.
Saurari rahotan Umar Faruk Musa domin cikakken bayani.
Facebook Forum