Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Salon Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa a Kenya


Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta
Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya karfafa yakin da yake na cin hanci da rashawa ta hanyar sanar da cewa za a binciki dukkan ma’aikatan gwamnati don gano hanyoyin da suke samun kudadensu.

Wannan sanarwa dai ta biyo bayan wata almundahana ne da ta girgiza kasar, inda aka gano cewa Miliyoyin dalolin Amurka sun bace a wasu ma’aikatun gwamnati da ake alakantawa da wasu jami’an gwamnati.

Shugaba Uhuru Kenyatta bayyana kansa a matsayin shugaba na farko da zai mika kansa a bincikeshi duk wani abu da ya mallaka, a kokarin gano gurbatattun jami’an gwamnati, yana mai cewa irin wannan bincike shine zai iya shawo kan barnatar da dukiyar gwamnati da ake yi. Yace jami’an gwamnati za a nemi dukkan ma’aikata su bayyana yaddda suka sami dukiyoyinsu, domin gano barayin gwamnati.

Shugaba Kenyatta ya ce “Dole ka gaya mana, wannan gidanka ne, kuma ga ainahin albashinka, ta wacce hanya ka sami kudin da ka iya sayen wannan gida? Wannan motar ka ce, ta ina ka samu kudin sayenta, kuma kar mutum ya saka sunan matarsa ko ‘ya ‘yansa a dukiyoyinsa, domin zamu gano cewa naka ne. Dole mutum ya bayyana inda ya sami dukiyarsa, kuma ni za a fara yiwa wannan bincike.”

A watan daya gabata, an bankado almundahana masu yawa da ta hada da ma’aikatan gwamnati a ma’aikatu masu yawa. Almundahanar da aka bankado ta kwarmata barayiin gwamnati da suka sace daruruwan miliyoyin dalar Amurka. Ya zuwa yanzu dai, an kama jami’an gwamnati sama da 40, ciki harda wasu ‘yan kasuwa.

Kenyatta ya ci gaba da nuna damuwarsa kan sace kudaden gwmanati da ake wanda ya wuce missali tun farkon hawa mulkinsa a shekarar 2013.

Yace “batun sace mutane suna sace dukiyar al’ummar Kenya, na rantse da Allah yazo karshe.”

Shugaban kasar ya ce wannan binciken da za a gudanar wani mataki ne ‘daya cikin matakan da aka dauka na kawo karshen satar kudaden gwamnati.

A farkon makon nan ne, shugaba Kenyatta ya bayar da umarnin cewa dukkan ma’aikatun gwamnati su bayar da cikakken bayani kan yadda suke sarrafa kudaden ma’aikatun daga 1 ga watan Yuli na wannan shekarar.

Ya ci gaba da cewa “alal missali, idan an gina wata hanya, muna son mu sani cewa, waye ya samu kwangilar? Kuma nawa ne kudaden kwangilar? Waye yazo na biyu da na uku a neman kwangilar? Me yasa aka baiwa mutum na farko kwangilar? Dukkan wadannan tambayoyi muna son jin amsarsu, al’ummar Kenya suna bukatar sani”

Ranar daya ga watan Yuni, shugaba Kenyatta ya bayar da umarnin a sake tantance dukkan shugabanin da ke kula da harkokin kudade. Ya kuma ce tantancewar zata hada da yin amfani da naurar gane idan mutun yayi karya dominn tabbatar da gaskiyarsa.

Kenya dai ta samu maki 28 cikin 100 a rahotan kungiyar dake yaki da cin hanci da rashawa ta Transparency International.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG