Lokacin da yake jawabi ga wani rukunin ‘yan sandan kwantar da tarzoma a birnin tarayya Abuja, babban Sufeto Janal Ibrahim Idris, ya ce aikin ‘yan sanda ne su tabbatar da cewa kowanne dan Najeriya ya bi doka da oda, kuma ‘yan sanda na sane da cewa babu wani mutum komai girmansa a kasar da ke sama da dokar kasa.
Sufeto Janal ya yabawa ‘yan sandan Najeriya bisa abin da ya kira jajircewarsu wajen aiki tukuru da kuma rage aikata miyagun laifuka a kasar.
Dakta Abubakar Umar Kari na jami’ar Abuja, ya ce bin doka da oda da kuma tsarin mulki na daga cikin ginshikan da aka kafa dimokaradiyya, kuma babu wata ‘kasa da zata iya zama lafiya har sai mutanen kasar baki daya suna bin doka da oda.
Sai dai kuma Dakta Abubakar ya ce a ‘yan kwanakin nan ana yiwa doka da oda karen tsaye, kuma don shugaban ‘yan sanda ya fito ya jaddada karfin doka da oda abu ne mai kyau, amma kuma wasu zasu kalla abin a matsayin yana gugar zana ne kasancewar yana rigima da wani hamshakin ma’aikacin gwamnati.
Shi kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Dakta Kabiru Danladi Lawanti, ya ce dangane da godiyar da Sufeto Janal ya ke yiwa jami’ansa abune da ya kamata. Amma maganar cewa aikata laifuka na raguwa a Najeriya, babu wani bayani da zai iya nuna hakan.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum