Tun shekara ta 2004 aka kafa kasuwar China Town, wadda gine-ginenta ya yi kama da irin wanda ake gani a birnin Sin. Kasuwar dai ta kunshi ginin shaguna kusan 200 da ake saye da sayarwa.
‘Yan Najeriya da ‘yan kasar China ne ke gudanar da harkokin saye da sayarwa, akasarin kayan da ake sayarwa sun kunshi kayyayakin da ake shiga da su daga China.
Sai dai kuma matsalar da tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta a ‘yan shekarun nan ya sa hada-hadar kasuwanci a cibiyar ya ja baya, har ta kai ga cewa wasu ‘yan kasar China sun rufe shagunan su sun koma wasu wurare.
Daya daga cikin wasu ‘yan Najeriya masu shaguna a China Town, Mallam Musa Danladi, ya tabbatar da cewa tabbas akwai masu shagunan da suka rufe harkokin kasuwancinsu suka tafi, kasancewar shagunan akwai tsada kuma hada-hadar kasuwanci ta yi ‘kasa.
Sai dai kuma bayanai sun nuna cewa bayan matakan tattalin arziki da aka dauka a Najeriya da kuma tsadar rayuwa da ta kawo nakasu a hada-hadar kasuwanci, a bangaren ‘yan kasar na Sin akwai wadanda ke zargin cewa harkokin irin na ‘yan danfara da Najeriya ta yi suna akai, na daya daga cikin dalilan da ya sa wasu ‘yan China ke gujewa harkokin kasuwanci a kasar.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin.
Facebook Forum