Tun cikin wannan makon ne aka fara samun kashe-kashe jifa-jifa a wadansu kauyuka, tare da sace-sacen dabbobi a sassa daban-daban na karamar hukumar Barikin Ladi.
Ranar Juma’a ne dai al’ummar Fulani suka zargi al’ummar Birom da sace wasu Fulani wadanda har ya zuwa yanzu ba a gano inda gawarwakinsu suke ba. Bayanai dai na cewa ya zuwa yanzu an kashe mutane masu yawa tare da kona wasu kauyuka dake yankin Barikin Ladi.
Mutanen yankin sun bayyanawa Muryar Amurka cewa suna jin ‘karan harbe-harbe kuma babu hanyar fita, kuma ya zuwa yanzu babu takamaiman adadin mutanen da suka rasa rayukansu.
Rikicin dai ya samo asali ne tsakanin Fulani makiyaya da Manoma, inda kowa ke zargin kowa da kai hari dake sanadiyar rayuka.
Jami’an tsaro dai sun shaidawa wakiliyar Muryar Amurka cewa ya zuwa yanzu dai ‘kura ta lafa, sai dai kuma wasu al’umomin Fulani da Birom baki ‘daya suna zargin jami’an tsaron da rashin daukar matakan da suka kama akan lokaci.
Domin cikakken bayani hirar Sarfilu Hashim Gumel da Zainab Babaji.
Facebook Forum