Kundin tsarin mulkin Najeriya na cike da dokoki masu ma'ana da la shakka in an yi amfani da su, za su tabbatar da adalci da galabar masu amana kan maciya amana.
Shirin “Arewa A Yau,” Ci gaban inda muka tsaya ne a makon jiya, inda za ku ji sauran sharhi ko ra’ayin Attahiru Baburawa kan kalaman batun odar makamai da mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Manjo Janar Babagana Monguno ya yi magana akai.
Masu gabatar da jawabai a taron kaddamar da wasu littattafai na adabi sun bayyana cewa yawan saki da ake yi a aure a Arewa, na daga cikin manyan dalilan da ke haifar da matsalar 'yan bindiga dadi da ma 'yan ta'adda.
Mako biyu kacal gabanin azumin watan ramadna na bana hijra 1442, malamai da sauran jama'a sun taru a dakin taro na masallacin tarayya a Abuja don kaddamar da faifan karatun alkur'ani mai girma izu 60 da Imam Abbas Uzairu Chikaji Zaria ya karanta.
Tashoshin dakatar manyan motoci sun fara aiki don rage yawan hatsari da ke faruwa a sanadiyyar gajiya da direbobi ke samu a Najeriya.
Ma'abota son a yi sulhu a matsayin mafita ga tabarbarewar tsaro a yankin arewa sun gudanar da wani taro a Kaduna.
Kalaman mai ba wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, da ya shafi tsoffin manyan hafsoshin soja kan batun rashin ganin makamai da aka sata da makudan kudaden da ake warewa ya janyo martani daga jama'a.
Muhawara ta sarke tsakanin gwamnatin Najeriya da jihar Delta da ke kudancin kasar kan hakkin kashe kudin da tsohon gwamnan jihar, James Ibori ya sace da Burtaniya za ta maido wa Najeriya.
Hadaddiyar kungiyar fataken abinci da dabbobi ta Najeriya, ta jaddada dalilinta na kin janye yajin kai abinci kudancin kasar.
Kwamitin jin Korafin Jama'a na Majalisar Waklilan Najeriya ya sake gayyatar mai kwarmato Dr. George Uboh kan bahasi na zambar kudin shiga sama da dala biliyan 25 daga kamfanonin man kasashen ketare.
Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta ce kimanin kashi 15-20% na Fulani makiyaya na Najeriya na ficewa daga kasar zuwa tudun mun tsira.
Yayin da ake ta korafe korafe a arewacin Najeriya game da zargin rashin kulawa da yankin, wasu 'yan yankin sun ce a gaya ma Shugaba Buhari cewa sun fa gaji da gafara sa, ba su ga ko kaho ba.
Yayin da ake haramar rantsar da sabon Shugaban Kasa a Amurka yau, masana na cigaba da fashin baki yayin da kuma sauran jama'a ke cigaba da bayyana ra'ayoyinsu kan wannan rana da kuma bukin.
Ana shirin rantsar da sabuwar gwamnati a Amurka, bayan zabe da aka gudanar a watan Nuwamban Bara.
A ci gaba da dauke hankalin duniya da abkawa Majalisar Dokokin Kasar Amurka da kuma tsige Shugaba Donald Trump karo na biyu da ya biyo baya, masana harkokin siyasar duniya na ci gaba da tsokaci game da tasirin wannan al'amarin.
Masana sun lura cewa ba za a yi sanyi a lokacinsa ba a Najeriya saboda dumamar yanayi, al'amarin da ya canza abubuwan da mutane su ka saba yi a lokacin na sanyi. Haka zalika, sun lura cewa hamadar Sahara na dannowa.
Bayan da 'yan Najeriya su ka yi ca, gwamnatin kasar ta janye shirin da aka yi zargin cewa karin kudin wutar lantarki ne a fakaice ta wajen rabewa da bangare mai zaman kansa.
Hukumar kula da farashin lantarki ta Najeriya ta ce kai tsaye ba ta kara farashin wuta da kashi 50 cikin 100 ba, amma an samu kari na wani kaso ga azuzuwan masu amfani da wuta biyar.
Kotu ta sake tura Omoyele Sowore, gidan jiran hukunci, akan zargin shi na tada zaune tsaye.
Wasu rahotanni na nuni da cewar sai da aka biya zunzurutun kudade kamun aka sako daliban Kankara.
Domin Kari