Yayin da a ka shiga shekara ta biyu a wa'adi na karshe na Shugaba Muhammadu Buhari, wasu 'yan arewa na cewa har yanzu ba su ga hakikanin baiyanar kahon da shugaba Buhari ya yi alkawari duk da dadewa a na gafara-sa.
Masu sharhin na magana kan irin alkawuran gyara da shugaba Buhari ya yi tun wa'adin sa na farko amma har yanzu ba a kaddamar da aiyukan zahiri ba a yankin arewa.
In za a tuna shugaba Buhari gabanin babban zaben 2019 ya yi alwashin mutane za su ga sauyi bayan nasarar dawo da Najeriya kan turbar da ya ce 'yan PDP sun kawar da kasar daga kan ta a tsawon mulkin su na shekaru 16.
Akalla dai akwai sauyin kawo wasu ministoci da shugaban ya yi da ajiye wasu kalilan da su ka gudanar da aiki a tsawon wa'adin farko, duk da akasarin ministocin sun zarce a tafiyar gwamnatin da ba ta faye sauye-sauye ba.
Dattijon arewa Alhaji Shehu Ashaka ya ce duk abun da areewa ba ta samu ba a mulkin shugaba Buhari zai yi wuya ta samu a wata gwamnatin.
Shi ma jigon APC Alhaji Bala Bello Tinka ya koka kan tafiyar hawainiyar aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kano.
Gabanin zaben 2023 da shugaba Buhari zai kammala wa'adi; a na muhawarar yankin da zai fi tagomashin karbar ragama da tunanin yankin yarbawa na sa ran samun ragamar, sai dai wasu 'yan arewa na cewa a'a a bar mafiya rinjaye su zabi wanda su ke so.