Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Delta Na Yunkurin Karbar Kudin Da Tsohon Gwamnanta Ibori Ya Wawure


Ibori
Ibori

Muhawara ta sarke tsakanin gwamnatin Najeriya da jihar Delta da ke kudancin kasar kan hakkin kashe kudin da tsohon gwamnan jihar, James Ibori ya sace da Burtaniya za ta maido wa Najeriya.

Gwamnatin jihar Delta na yunkurin karbar kudin da Burtaniya za ta dawo da su Najeriya da tsohon gwamnan jihar James Ibori, wanda ya sace, ya boye a kasar da ta yi wa Najeriya mulkin mallaka.

Tsohon gwamnan dai ya yi nasarar kauce wa shari'a a Najeriya, amma Burtaniya ta kama shi da laifi har ta tura shi gidan yari a shekarar 2012.

"Wannan shi ne kason farko na kudin da za mu dawo da su Najeriya da barayin biro su ka boye a Burtaniya a karkashin wata yarejeniya da mu ka cimma a shekarar 2016," Inji jakadiyar Burtaniya a Najeriya, Catriona Laing a taron sanya hannu don dawo da kudi fam miliyan 4.2 da tsohon gwamnan Ibori James ya boye a Burtaniya, kwatankwacin Naira biliyan 2.4.

Ministan Shari'a na Najeriya, Abubakar Malami ya ce za a yi amfani da kudin ne wajen kammala ayyukan hanyoyi don amfanin 'yan Najeriya.

Shugaban riko na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya ce ayyukan hanyoyin da a ke gudanarwa yanzu, tun a zamanin da ya shude aka sace kudin aikinsu.

Shi kuma babban lauyan kare hakkin 'yan adam, Femi Falana, cewa ya yi bai dace gwamnatin Najeriya ta kashe kudin ba.

"Gwamnatin tarayya ba ta da hurumin kashe wadannan kudade kuma Burtaniya ba ta da ikon cewa ga abin da za a yi da kudin, kamata ya yi ma a tilasta wa bankunan da su ka boye kudin su biya al'ummar jihar Delta hatta kudin ruwa na kudin da a ka sace," Inji Falana a zantawa da gidan talabijin na Channels.

Tsoron masu sharhi shi ne guje wa sake karkatar da irin wannan kudi daga masu almundahanar jiya zuwa masu almundanar yau, wato “ja ya fado ja ya dauka.”

Saurari rahoton Nasiru Adamu Elhikya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG