Makiyayan na daukar matakin don samun inda za su zauna da dabbobin su da kuma tsira da rayukan su.
A wani taro da Sultan Muhammad Sa'ad a Abuja, kungiyar ta kara da cewa makiyayan na daga cikin wadanda miyagun iri da su ka hada da wasu Fulani kan sace don samun kudin fansa, inda hakan kan sa makiyayan sayar da shanun su domin karbo 'yan uwan su.
Sakataren kungiyar, Baba Ngilzerma, ya ce kimanin makiyaya dubu goma ne su ka rasa ran su a fitintinu a Najeriya, hakanan fiye da shanu miliyan uku a ka sace mu su.
Kungiyar ta bukaci gwamnati ta kawo wa Fulani makiyaya dauki wajen samar mu su kudin tallafi, wajen kiwo da makaranta don 'ya'yan su, domin su samu ilimin adddini da na zamani da kuma kare su daga barayin shanu da mutane.
Sultan Muhammad Sa'ad ya ce sam ba daidai ba ne yadda a ke yi wa Fulani ko makiyayan su kudin goro da nuna duk miyagu ne da za a iya cafke kowannen su a aika lahira.
Sultan ya kara da cewa lamarin ya kai matsayin da sai kowa ya shigo lamarin don a gyara yadda a ka bata sunan Fulanin da hakan ka iya shafar mutuncin kakanni ta fuskar taribiyya da adddini.
Sutlan ya bukaci Fulani su kawar da miyagun iri a tsakanin su da sanin dabarun zamani na yin kiwo.
A makonni baya bayan nan dai ana kai wa Fulani da basu ji ba ba su gani ba hare-hare a sassan Najeriya, saboda zargin da ake wa wasu fulani na satar mutane domin neman kudin fansa, inda shugabannin fulani da na al’uma a Najeriya suka yi kira da gwamnati da ta tashi tsaye wajan magance wannan matsala da ta kunno kai.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya: