Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saboda Dumamar Yanayi, Ba Za a Yi Sanyi Bana Ba Sosai a Najeriya


Canjin Yanayi
Canjin Yanayi

Masana sun lura cewa ba za a yi sanyi a lokacinsa ba a Najeriya saboda dumamar yanayi, al'amarin da ya canza abubuwan da mutane su ka saba yi a lokacin na sanyi. Haka zalika, sun lura cewa hamadar Sahara na dannowa.

A bisa yanda a ka saba, sanyi kan shigo sosai daga watan Disamba zuwa Janairu, kafin Maris, inda yanayin zafi na damana ke shigowa

Tuni wannan sauyin ya shafi masu cin kasuwar rigunan sanyi inda ba sa samun ciniki don ba matukar bukatar hajarsu.

Masanin yanayi Hussaini Jar Kasa ya ce sare bishiyoyi, hayaki daga motoci da masana'antu da ma kona dazuka ko share su don gine-gine da gonaki ne ya ta'azzara lamarin.

Illar wadannan lamura masu bata yanayi sun shafi malafar duniya (wato "ozone layer") da kan rage zafin rana.

Hakanan illar inji Jar kasa ta rage yawan tsuntsaye masu tasowa tun daga Turai zuwa mafi ni'imar waje na kogin Hadeja a jihar Jigawa.

Shugaban Hukumar Hasashen Yanayi na Najeriya, Farfesa Sani Mashi ya ce Najeriya na da kwarewa a lamuran bincike kan sauyin yanayi.

Face an samu matakai na kare lafiyar yanayi, za a ci gaba da samun sauye-sauye masu tada hankali.

Ga cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00

Karin bayani akan: Dumamar Yanayi, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG