A daidai lokacin da Majalisar Wakilan Najeriya ke jiran bayyanar shugaban kasa gabanta yau Alhamis, domin amsa tambayoyi game da halin tabarbarewar tsaro da kasa ke ciki, Ministan Shari’a ya ce bayanin Buhari ga Majalisa na iya amfanar ‘yan bindiga
Shahararren mai kwarmaton nan na Najeriya, Dr. George Uboh, ya sami gayyatar Majalisar Wakilan Najeriya don ba da bahasi kan zargin salwantar kudi sama da dala Biliyan 35 a ma'ajiyar gwamnatin tarayya.
Yayin da gwamnatin Najeriya ke nazarin yiwuwar sake bude kan iyakarta don hada hadar cinakayya da sauransu, 'yan kasar sun shiga muhawara kan alfanu da kuma rashin alfanun yin hakan.
Mako daya bayan sace daliban sashen Faransanci na jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria su tara,da wasu mutane da masu satar mutane su ka yi a hanyar Kaduna zuwa Abuja, an samu nasarar sako su bayan biyan kudin fansa.
'Yan bindigar da suka sace daliban Sashen Harshen Faransanci na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Lahadi, na neman kudin fansa Naira miliyan 450 daga wajen ‘yan uwan daliban.
A cigaba da tattaunawa da 'yan Najeriya ke yi kan matsalar kuntata ma jama'a da 'yan sanda na musamman kan yi, an bukaci a yi garanbawul ma tsarin aikin 'yan sanda gaba daya, ba SARS kawai ba.
Tun rasuwar marigayi mai yaki da miyagun barayi, Alhaji Ali Kwara a ke ci gaba da nuna juyayin rashin sa, inda kafafen sadarwar yanar gizo su ka cika makil da ta'aziyar rasuwar mutumin da a ke aiyanawa a matsayin mai Jarumi.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya ce yana jagorantar wani shiri na tattara bayanan asarar rayuka da dukiya da al'ummar arewa suka yi don neman diyyar da ta kai Naira tiriliyan bakwai.
Kungiyoyin tallafawa marayu da zawarawa da su ka hada da matan da mazajen su su ka rasu, karkashin inuwar kwamitin marayu na JIBWIS, sun yaye matan da a ka koyawa sana'a don dogaro da kai.
Ambaliyar ruwa mai tsanani da ta shafi musamman wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya wansa shi ne mafi yawan jama'a, ya kawo fargabar yiwuwar a samu karancin abinci, saboda yanda ruwan ya shafe gonaki ya maida su tamkar kananan koguna.
Shugabar hukumar bunkasa zuba jari a Najeriya (NIPC) Yewande Sadiku, ta ba da tabbacin aiki da hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa wajen samun rage haraji don kara janyo hankalin masu zuba jari su ci gaba da shigowa Najeriya.
Majalisar Limaman birnin Abuja ta gudanar da gagarumin taro don karfafa Limamai gwiwa su ci gaba da tsayawa kan gaskiya tare da gujewa marawa wani bangaren siyasa baya.
Duk da matsin tattalin arziki da yawan sanyin guiwa da ‘yan Najeriya ke nunawa, hakan bai hana gwamnatin da jama’a daukar cika shekaru 60 da samun ‘yanci abu mai muhimmanci ba.
Hukumar zaben Najeriya ta ce gayyaci kamfanoni don kera na'urar da ta dace da nufin komawa kada kuri'a nan gaba ta hanyar na'ura mai kwakwalwa.
Kungiyar Kwadagon Najeriya ta NLC da gamayyar kungiyoyin kwadago ta TUC, sun janye yajin aikin gama-gari da suka shirya shiga yau Litinin, 28 ga watan Satumban shekarar 2020, akan karin farashin man fetur da wutar lantarki.
An shiga jajiberin ranar da kungiyar kwadagon Najeriya NLC za ta auka yajin aiki da ma zanga-zanga don matsawa gwamnati lamba ta janye karin farashin fetur da lantarki da ta yi da tuni hakan ya fara tasiri a kan farashin kayan masarufi.
Hukumar kula da rayuwar dabbobi ta Majalisar Dinkin Duniya da masu kare hakkin dabbobi na Afirka, sun nuna damuwa ga yadda Jakuna ke matukar raguwa a duniya, saboda kashe su da a ke yi don samun nama da kuma amfani da fatar su wajen magani a kasar China.
Kungiyar tattaunawa tsakanin Musulmi da Kirista ta “Interfaith Dialog for Peace” ta ce kauce wa kiyayyar addini da kabilanci ne zai kawo zaman lafiya mai dorewa a jihar Kaduna.
Bayan shafe shekaru masu yawa a yaki da cutar shan inna, hukumar lafiya ta duniya ta ayyana Afrika a matsayin nahiyar da ta barranta daga cutar shan inna bayan Najeriya ta samu shekaru 4 ba tare da bullar cutar ba.
Domin Kari