An cigaba da samun martani bayan labarin da Jaridar "Wall Street Journal" ta Amurka ta wallafa, labarin da ke nuna an biya diyyar naira miliyan 344 kafin sako yara 344 'yan makarantar sakandaren Kankara, kafin aka sake su daga hannun masu satar mutane.
Wannan dai ya nuna an fanso kowanne yaro daya daga yaran a kan Naira miliyan daya kenan.
Labarin zai zama ya saba da bayanan hukumomin Najeriya da ke cewa ba a ba da ko sisin kobo ba gabanin sako daliban.
Hakanan labarin ya nuna daliban sun zauna cikin ukuba da cin danyen dankali da ganyen kalgo mai daci.
Kazalika yaran sun zauna a wurare masu macizai da kunamu kafin nasarar samun komowa gida.
Gwamnatin Najeriya ta ce an sako yaran ne lami lafiya ba tare da musayar kudi tsakanin hukuma da miyagun irin ba.
Ministan labarun Najeriya Lai Muhammed ya ce, sam ba a yi musayar kudi ba, kuma tattaunawar an yi ta ne kamar yadda a ke yi a sauran sassan duniya, an dai sako daliban ba tare da gindaya wani sharadi ba.
Alkali a kotun sasanci ta jihar Katsina Barista Sabi'u Jibiya ya nuna tababa ga matsayar gwamnati kan cewa ba a ba da kudin fansa ba.
Barista Jibiya ya zaiyana yanayin Najeriya a yanzu da labarin "Gandun Dabbobi" na littafin nan "Animal Farm" da George Orwell ya wallafa.
Shi kuma dattijon kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah, Dodo Oroji ya ce ko ma dai yaya a ka yi, sulhu da jagororin masu satar zai kawo maslaha.
Hakika sace daliban Kankara ya kara sa sunan Kankara ya yi fice a kafafen labaru, da sanya daliban a cikin tarihi don shugaban kasa da kan sa ba ma kansilan anguwar sakandaren ba ya zo ya yi mu su jawabi.
Ga rahoton da Nasiru Adamu El-Hikaya ya hada muna a cikin sauti.