A yau dinnan gwamnatin 'yan jam'iyyar Dimokrats ta ke dawowa kan mulki bayan samun wa'adi daya na tsawon shekaru hudu na 'yan jam'iyyar Republican karkashin Shugaba na 45, Donald Trump.
Za a iya cewa an samu sauyi mai sauri na zakudawar Republican ba kamar yanda ya faru ga tsohon shugaba George W Bush, wanda ya yi mulki na tsawon shekaru 8, inda Dimokrats ta karba a 2009 da samun Shugaba Barack Obama, wanda shi ma ya samu wa'adi na biyu.
Masu nazari, 'yan siyasa da ma kusan duk wata majalisar hira a Najeriya na duba yanda Shugaba Donald Trump ya fice daga fadar White House kuma ba tare da jira don tarbar sabon Shugaba ba, kamar yanda Shugaba Obama ya yi ma sa a 2017.
Ga ra'ayin kwamishinan lafiya a yankin arewa maso gabas, Dr. Ahmad Gana, wanda ya yi hulda da hukumomin lamuran lafiya na Amurka. Shin me Dr. Gana zai ce kan nuna sanyin guiwar Trump ko akasin hakan a daidai lokacin da ya bar gado ba da shiri ba? Dr. Gana ya ce ga dukkan alamu har yanzu Trump na ganin da magudi aka zabi Biden wanda don haka ne ma ya ki yin masa maraba lale.
Su ma 'yan jarida na baiyana ra'ayin da ya sha bamban da wasu masu sharhin da nuna ko banza za a ga gurbin Trump. Yusuf Ishaq Baji daya ne daga shugabannin rediyon vision a Najeriya, kuma ya bayyana irin wannan ra'ayin.
Duk da tsarin dimokradiyya na ba da dama mutane su zabi wanda su ke so, har yanzu tsarin bai fara karfi ba a wasu kasashe musamman na Afurka inda wasu shugabanni ke amfani da sunan dimokradiyya su na yin mulkin iya rai iya fama.
Ga Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton: