Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da gwamnatin Najeriya a ta bakin mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno, ke nuna dawowa daga rakiyar sulhu da wadanda gwamnatin ke dauka a matsayin abokan gaba.
Janar Monguno ya ce, ba za a yi sulhu da miyagun iri ba, kawai murkushe su za a yi, da hakan ke nuna gwamnati ba ta ga amfanin sulhu da masu rike makamai ba da ya kai ga shugaba Buhari ma ya ba da umurnin bude wuta ga duk wanda a ka gani da bindiga a daji ba tare da bin ka'idar doka ba.
Taron dai zai hada da makiyaya da wasu da lamarin tsaro ya taba shafa inda za su karfafa batun zama don tattaunawa da wadanda su ka dau makamai don kwance mu su damarar fada ta lalama da yiwuwar samun diyya.
Duk da ba cikekken bayani kan taron, amma daya daga mahalarta taron makiyayi Abubakar Usman Shumo ya ce Dr. Ahmed Gumi ne ya gayyaci jama'a da za su yi kokarin jan ra'ayin hukuma ta sake gwada sulhun ta hanyar tattaunawa da wadanda su ka zama baragurbi.
Haka nan Shumo ya nuna damuwa ainun ga yanda masu satar mutane su ka koma sace dalibai a makarantu da ya ce hakan babban barazana ce ga cigaban ilimi a yankin arewacin Najeriya.
Shugaban rundunar adalci Abdulkarim Daiyabu ya ce dalilai na tsawon shekaru su ka haddasa tabarbarewar tsaron da sai an zauna a gano bakin zare.
Wani abin damuwa shi ne yadda kalubalen na tsaro ya shiga wani sashe a jihar Kebbi inda akalla a ka sace wata mata a yankin karamar hukumar Kalgo kazalika da samun 'yar tsama tsakanin Fulani makiyaya da wasu masu shigen sintiri.
Ga rahoton da Nasiru Adamu El-Hikaya ya hada a cikin sauti.