Kungiyar ta ce tana nan daram kan bakarta, har sai an biya diyyar mutane da dukiyoyi da a ka salwantar mata.
Wannan shi ne mataki mafi tsauri da fataken suka dauka wadanda akasari 'yan arewacin kasar ne, a kan asarar rayuka a hargitsin kasuwar Sasa a Ibadan da kuma lokacin zanga-zangar endsars.
A taro da manema labarai a Abuja, shugaban kungiyar fataken Dr. Muhammad Tahir, ya ce an dade ana kashe mutanensu, da lalata dukiyoyinsu a yankin kudu, amma ba wanda ya jajanta musu ko bin kadinsu kan wannan asarar.
Dr.Tahir, ya ce sun kafa shingayen dakatar da duk wani mai karambanin zullewa da kayan abinci zuwa kudu.
Sun ba da umurnin hana duk wata mota motsawa da kayan abinci, musamman bayan samun labarin masu yunkurin amfani da filin tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano, don jigilar kayan abincin.
Da ya ke sharhi kan lamarin kasuwancin fataken, Talban Bauchi Tahir Ibrahim Tahir, ya ce ya na da kyau 'yan kasuwar su dakata daga zuwa kudu da samun wata babbar kasuwar fatake a arewa.
A na iya sauraren cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya, a cikin sauti.