Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Jajibirin Rantsar Da Sabon Shugaban Amurka Joe Biden


Joe Biden da Kamala Harris
Joe Biden da Kamala Harris

Ana shirin rantsar da sabuwar gwamnati a Amurka, bayan zabe da aka gudanar a watan Nuwamban Bara.

Yayin da a ka shiga jajibirin rantsar da shugaban Amurka na 46 Joe Biden, masana na kara fashin baki kan sauye-sauye da a ke sa ran samu a fadar "White House."

Har zuwa kwana na kusa da karshen mulkin gwamnatin shugaba Trump mai barin gado, gwamnatin na cigaba da aiwatar da ayyuka na matakai masu tsauri, musamman kan kasar Iran da Amurka ke zargin ta ki daina daukar matakan kera makaman kare dangi.

Masana kimiyyar siyasa sun ce Trump a yanzu na cijewa wajen nuna ki-fadi na rashin nasarar zabe, amma sai bayan ban kwana da madafun iko zai shiga yanayin juyayi ko akasin haka na rashin cimma burin zarcewa kan mulki.

Masanin kimiyyar siyasa na jami'ar Abuja Dr. Farouk BB. Farouk, ya ce Trump ya gudanar da mulki bisa muradun da su ke zuciyar sa ne.

Shin me zai faru ga Donald Trump a lamuran sa na tsohon shugaba?.

'Yan siyasar Najeriya na fadar irin sauyin da su ke hasashen sabon shugaba Biden zai kawo; da ya hada da yaki da dumamar yanayi, da rage kyamar bakar fata.

Sani Gwamna jigo ne a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya. Cewa ya yi Joe Biden da zai cika shekaru 78 a watan Nuwamba, shine mafi tsufa a shugabannin Amurka a lokacin hawa karagar mulki.

Kafin zuwan Biden Trump ne mafi tsufa da ya hau mulki ya na mai shekaru 70, wanda shi kuwa shugaba Ronald Reagan da ya hau yana da shekaru 69.

Marigayi tsohon shugaba Theodore Roosevelt ne ya fi yarinta zuwa yanzu don ya hau ya na mai shekaru 42.

Mafi rashin dadewar shugabannin Amurka a kan gado da a baya a ka dauka ya fi tsufa a shekaru 68 a 1841 shi ne shugaba William Henry Harrison wanda ya yi kwana 32 kan mulki, Allah ya yi ma sa rasuwa sanadiyyar rashin lafiya.

Sai a saurari rahoton a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG