Masanan sun ce lamarin kan kara ta’azzara ne idan aka bar matan da da aka saka da yara ba tare da taimako ko matakan tarbiya ba, wanda hakan kan jefa rayuwar yaran a hannun bata gari.
Mai bitar daya daga littattafan mai taken "Sarkakiya" Rahma Abdulmajid, ta ce akasarin sakin aure ba ya kula da abin da zai biyo baya da kan shafi kananan yaran da aka haifa.
Haka nan tsohuwar miniatar ilimi 'Yar majalisar Wakilai a yanzu Aishatu Jibir Dukku, ta ce mata kan shiga yanayin garari in aurensu ya mutu da yara a tsakani.
Ita kuma babbar bakuwa uwar gidan gwamnan jihar Neja, Hajiya Amina Abubakar, ta ce in an baiwa mata dama za su yi amfani da basirarsu wajen saita al'umma da kawo ci gaban kasa.
Marubuciyar littafin Mairo Mudi ta ce za a ci gaba da irin wannan taro don fito da darussa masu amfani.
Taron dai an gudanar da shi ba kida ko waka sai wakokin baka da fasaha da 'yar marubuciyar ta gabatar.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.