A ranar Litinin din nan ne gamayyar kungiyoyin kwadagon Najeriya na NLC da TUC ke aukawa ckin wani gagarumin yajin aiki.
Hukumar yaki da cin hanci EFCC ta ce ta na sane da wani faifan bidiyo da a ka ga wani gwamna na watsa wa magoya bayansa kudi.
Hukumar kare hakkokin masu sayen kayayyaki ta Najeriya ta FCCPC na shirin rufe wani shagon ‘yan kasar China da ke Abuja, wanda rahotanni suka bayyana cewa yana nuna wariya ga 'yan Najeriya.
Iyayen 'yan matan Chibok sun bukaci a raba wasu daga cikin 'ya'yansu da a ka kubutar da tubabbun mazaje 'yan Boko Haram da ke zama da su a Borno karkashin kulawar gwamnati.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara nazarin rahoton babban mai bincike ayyukan Bankin CBN ya gudanar a zamanin mulkin Buhari.
'Yan kungiyar Shi'a almajiran Sheikh Ibrahim Elzazzaky sun gudanar da zanga-zangar marawa Falasdinawa baya kan yakin Gaza a sassa daban-daban na arewacin Najeriya.
Bisa yanda canjin dala ke hawa da sauka, hukumar alhazan Najeriya ta ce duk wanda zai biya kujera yanzu zai bada daga Naira 8, 254, 464 a arewa sai Naira miliyan 8, 454, 464 a kudu.
Gwamnatin Najeriya ta ayyana mawallafin jaridar DESERT HERALD Tukur Mamu a jerin mutanen da ta ke tuhuma da daukar nauyin ta'addanci a Najeriya.
Wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta yi watsi da daukaka karar bukatar sako bayanan kadarorin tsofaffin shugabannin Najeriya, da suka hada da Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari da mataimakansu Namadi Sambo da Yemi Osinbajo.
Kungiyoyinn Fulani makiyaya sun yi gagarumin taron neman bakin zaren dawo da martabar su a idon duniya daga kashin kajin da wasu ke shafawa mu su.
Hargitsi ya barke a babbar kasuwar Abuja wato Wuse bayan da 'yan sanda su ka bude wuta da ya kai ga mutuwar wani dan kasuwa.
'Yan kasuwar canjin kudi da dama sun nuna rashin gamsuwa da soke lasisin sama da kamfanonin canji 4000 da babban bankin Najeriya CBN ya yi.
Babban Bankin Najeriya CBN ya soke lasisin wasu kamfanonin canjin kudi 4,173, cikin kimanin 5000 da ake da su.
Najeriya ta amince da dawo da hasken wutar lantarki ga jamhuriyar Nijar bayan janye wasu takunkumai da Kungiyar Raya Tattalin Arziki Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, ta yi kan kasar.
Yayin da talakan Najeriya ke ci gaba da dandana kudarsa, hankula na dada karkata kan rawar da tashin farashin dala ke takawa.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu ya ce ba lalle sai an kafa kotuna na musamman ba don sauraron shari'un cin hanci da rashawa.
Tsohon gwamnan jihar Yobe Sanata Bukar Abba Ibrahim ya rasu yana da mai shekaru 75.
Hukumar alhazan Najeriya (NAHCON) ta ayyana farashin kujerar hajjin bana da ya doshi Naira miliyan 5.
Bayan shafe dare da wuni daya su na yajin canjin kudi, 'yan kasuwar canji a Abuja sun tsaida shawarar janye yajin don komawa aiki a yau jumma'a.
Domin Kari