Wannan dai na zuwa ne biyo bayan shirin wasu matasa na gudanar da gagarumar zanga-zanga don nuna damuwa kan dan karen tsadar abinci da sauran kayan masarufi a kasar.
Abinda ya fi tsananta kalaman malaman akan zanga-zangar shi ne furucin wani matashi da ke cewa a ingije malami daga kan mumbari matukar ya hana gudanar da zanga-zangar.
Wani limami a Kaduna Malam Sunusi Khalil, na daga cikin wadanda su ka fi fusata kan bijirewa malamai masu kin jinin zanga-zanga.
Duk da cewa an samu malaman da su ka dauki matakin tsaka-tsaki a kan batun zanga-zangar, kai tsaye wasu na cewa halal ne a irin yanayin da Najeriya ke ciki yayin da wasu ke cewa haram ne.
Farfesa Mansour Ibrahim Sokoto, na daga cikin malamai masu nuna rashin dacewar zanga-zanga, saboda ba za ta haifar da alheri ba a cewarsa. Ya ce malamai da yawa basa goyon bayan zanga-zanga saboda ba a cika gamawa lafiya ba, kuma duk abinda zai kawo zubar da jini ko asarar dukiya, ba zai taba zama halal a addinin musulunci ba.
Amma shaharerren malamin Islama Dokta Ahmad Gumi, ya ce zanga-zanga ce yaren da gwamnati ke ji. Ya kuma lura cewa da alama gwamnatin Tinubu na fahimtar abubuwa ta kuma dauki mataki. Sai dai ya ja hankalin matasan da su guji wuce gona da iri a lokacin zanga-zangar.
A sharhinsa Farfesa, Sadik Umar Gombe, ya ce jigon dimokradiyya ne gudanar da zanga-zangar lumana.
A cibiyar kasuwancin arewa wato Kano, sakataren majalisar hadin kan malamai Dr. Sa’idu Dukawa, ya kawo maslahar da ta hada da addu’a da sama wa matasa ayyukan yi. Yana mai cewa ya kamata gwamnati ta dauki matakan gaggawa don inganta rayuwar matasa, da samar da fahimtar juna wajen kawo sauki ga al’umma.
Za a jira zuwa karshen wata don ganin yiwuwar wannan zanga-zanga wacce a tsarin kururuwarta ta,za a iya kwatanta ta da zanga-zanagar yaki da zargin zaluncin ‘yan sandan SARS a zamanin tsohuwar gwamnatin Buhari.
Dandalin Mu Tattauna