Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masharhanta Sun Bayyana Mabambantan Ra’ayoyi Kan Shirin Zanga-Zangar Matasa


Baba Usman Ngelzarma a taron kungiyar Myetti Allah
Baba Usman Ngelzarma a taron kungiyar Myetti Allah

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum da kuma wasu shugabannin al’umma na bayyana ra’ayoyi mabambanta kan shirin zanga-zanga da matasan Najeriya ke yi don nuna damuwa kan tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar.

Wannan dai na zuwa ne gabanin zanga-zangar da matasan kasar suka shirya yi ranar Alhamis daya ga watan Agusta.

A zantawarsa da Muryar Amurka, shaharerren malamin Islama Dr. Ahmad Gumi, wanda a baya ya ce zanga-zanga ce yaren da gwamnati ke ji, a yanzu ya bukaci matasan su jinkirta zanga-zangar, ya ce da alama sakon matasan ya isa ga hukumomin gwamnati.

Sheikh Ahmad Gumi
Sheikh Ahmad Gumi

“Babu wata doka da ta hana mutun ya bayyana rashin jin dadinsa a kan abubuwan da ke faruwa kuma ya nemi a yi sauyi, amma a yanzu ba lokacin yin zanga-zanga ba ne saboda halin da kasar ke ciki,” a cewar Gumi.

Malamin ya kara da yin kira ga matasan da su janye maganar zanga-zanga gaba daya, su ba gwamnati zuwa wata 6 ko zuwa watan Janairu su gani idan ba ta yi wani abu ba, to sai su shirya zanga-zangar lumana.

Shi ma shugaban kungiyar makiyaya ta Myetti Allah, Baba Usman Ngelzarma, ya shawarci matasan da su janye zanga-zangar saboda da alama ba za ta haifar da alheri ba.

Tsohon kwamishinan harkokin kasuwanci na jihar Sokoto Aminu Bello, ya yi kira ga gwamnati da ta biya wasu bukatun matasan don dakatar da shirin zanga zangar.

Zanga-zanga a Kenya
Zanga-zanga a Kenya

“Muna kira ga gwamnati da ta duba halin da ake ciki, ba maganar cire tallafin man fetur ba ne kadai, amma a rage kudin mai, a dauki matakin saukar da farashin dala, sannan a rage haraji, to idan a ka yi haka ta kowane bangare za a samu sauki,” a cewar Bello.

A nasa bangaren shugaban gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya, Jamilu Aliyu Charanci, ya nemi a kwantar da guguwar da ke tasowa kar ta kai ga juyin-juya hali duba da halin da ake ciki.

Jamilu Aliyu Charanci na kungiyar CNG
Jamilu Aliyu Charanci na kungiyar CNG

Yanzu dai da alamun wasu matasan sun janye daga zanga-zangar inda wasu ke cewa ba gudu ba ja da baya.

Saurari rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:

Masharhanta Sun Bayyana Mabambantan Ra’ayoyi Kan Shirin Zanga-Zangar Matasa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG