Wannan na zuwa ne daidai lokacin da hukumar ke shan alwashin gurfanar da duk wanda a ka samu da wulakanta Naira gaban kotu.
Jami'in labarun EFCC Dele Oyewole ke ba da tabbacin sun ga bidiyon gwamnan da ke yawo a yanar gizo kuma su na nazarin faifan don daukar matakin da ya dace.
A nan ba mamaki EFCC ka iya tura takardar gargadi ga gwamnan don a yanzu ba za ta iya gurfanar da shi gaban kotu ba don kariyar da ya ke da ita "babban laifi ne wulakanta Naira don haka za mu cigaba da daukar mataki kan duk wanda ke keta haddin Naira "
Gurfanar da wanda ya sauya jinsi zuwa mace BOBRISKY da EFCC ta yi gaban kotu don liki da Naira har kotu ta daure shi wata 6 ya jawo sukar EFCC cewa matakin ka iya takaita kan wadanda ba su da tagomashi a madafun iko don watsa Naira dabi'ar wasu daga manya ne a Najeriya.
Dan canjin kudi da ke mu'amala da takardun kudi kullum Alhaji Sani Imam Dogon Daji ya ce laifin ya shafi ajin 'yan jari hujja ne.
Tsohon mamba a hukumar raya irin Ibrahim Musa ya yaba wa EFCC don matakin da ya ce zai tilasta wasu samun kishin kasa.
Dan siyasa Abacha Ibrahim Jalingo na da ra'ayin yin takatsantsan wajen daukar matakin gabanin gagarumin aikin wayar da kan 'yan kasa duk da matakin tauna tsakuwa ne.
EFCC ta fitar da sanarwar za ta shiga farautar masu wulakanta Naira a bukukuwa, kulob-kulob da sauran wajajen shagali.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:
Dandalin Mu Tattauna