Alhazai na rike da lema wasu na neman duk inda inuwa ta ke don fakewa yayin da wadanda su ka zauna a tantuna ke amfana da wasu na’urorin da ke buso iska don rage zafin.
Babban likitan alhazan Najeriya Dr. Abubakar Adamu Isma’il ya bukaci alhazan su yawaita shan ruwa ya na alwashin su na da kayan aikin ko-ta-kwana don kula da wadanda ya zaiyana da gubar rana ta yi wa illa “za mu kula da wanda gubar rana ta shafa ta hanyar shayar da shi ruwa ko ma kwantar da shi a motocin daukar marar sa lafiya masu sanyi da ma yi wa majinyaci karin ruwa har sai ya farfado.”
Zafin rana dai a Saudiyya ba bakon abu ba ne kasancewar kasar na yankin hamada da kuma yanzu da sassan duniya ke fuskantar karin dumamayar yanayi.
Sheikh Abdulsalam Baban Gwale na daya daga alhazai kuma ya zauna a kasar na tsawon shekaru yayin da ya ke karatu a jami’ar Madina “zafin Saudiyya na daban ne da kan sa mutane su yi ta zubar da zufa kuma a kan ba da sanarwa na bayanan zafin don mutane su dau matakai. Motoci ma na fasinja sai masu inganci da na’urar sanyi a ke bari su hau titi.”
Ko da akwai kalubale irin na zafin rana, amma dan majalisar wakilai na taraiyar Najeriya da ke kwamitin lamuran aikin hajji Sada Soli Jibia ya ce a kan samawa alhazai masaukai masu ma’ana.
Da zarar an sauka daga arfa za a nufi filin Muzdalifa inda za a kwana daga nan za a fara jifar shaidan da bukin babbar sallah.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El Hikaya cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna