Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Mamu A Jerin Masu Daukar Nauyin Ta'addanci


Tukur Mamu
Tukur Mamu

Gwamnatin Najeriya ta ayyana mawallafin jaridar DESERT HERALD Tukur Mamu a jerin mutanen da ta ke tuhuma da daukar nauyin ta'addanci a Najeriya.

Mamu wanda sunan sa ya fito a jerin mutum 15 da a ka zaiyana da alaka da 'yan ta'adda; na hannun rundunar tsaron DSS tun 2022 yayin da a ka kama shi kan hanyar tafiya umrah.

An zargi Tukur Mamu wanda ya yi fice a shiga tsakani don sako wadanda 'yan ta'adda su ka sace a harin jirgin kasa tsakanin Abuja da Kaduna, da ba 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane Dala 200,000 a matsayin kudin fansar wadanda a lokacin a ka yi awon gaba da su bayan bindige kimanin mutum 50.

Yan Bindiga
Yan Bindiga

A hirar ta da Muryar Amurka, Zainab Mamu 'yar Tukur Mamu ta ce ta yi asarar rubuta jarrabawar karshe ta aikin likita a jami'ar MUST ta kimiyya da Fasaha da ke Masar lokacin da labarin sabuwar tuhumar da a ke yi wa mahaifin su ta bayyana cewa, "Na kasa rubuta jarrabawar karshe don tashin hankali da ciwon damuwa kan wannan labarin. Mu na kira ga shugaba Tinubu da mataimakin shugaba Kashim Shettima su taimaka a ba da belin mutumin da a ka sani in ya so sai a cigaba da shari'a. Yanzu haka ba shi da lafiya. "

Shaharerren mai sharhi mazaunin Kaduna wanda ke da masaniya kan lamuran kama Tukur Mamu Mahdi Shehu ya ce lokaci ya wuce kimar da ya dace a kammala irin wannan binciken.

In za a tuna lokacin da lamarin ya auku tsohuwar gwamnatin Buhari ta kafa kwamitin mutum 7 don karbo wadanda ke dajin.

Sanarwar ta gwamnati daga hukumar bayanan sirri na hada-hadar kudi NFIU ta ce Mamu na daga mutane 9 da kuma wasu masu kamfanonin canji 6 da ke daukar nauyin ayyukan ta'addanci musamman na Boko Haram da ISWAP.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG