Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Albashi Mafi Karanci: Da Babu Gara Ba Dadi - TUC/NLC


Zanga-zangar tsadar rayuwa da NLC ta gudanar a Abuja
Zanga-zangar tsadar rayuwa da NLC ta gudanar a Abuja

Shugabannin kwadagon sun bayyana matsayar gabanin gabatar da tayin ga majalisun kwadagon don gamsar da su amincewa da hakan ya fi a’ala.

Gamayyar kungiyar kwadagon Najeriya ta ce tayin Naira 70,000 da shugaba Tinubu ya yi a matsayin mafi karancin albashi da babu ne gara ba dadi.

Shugabannin kwadagon sun bayyana matsayar gabanin gabatar da tayin ga majalisun kwadagon don gamsar da su amincewa da hakan ya fi a’ala.

Wannan dai na nuna a karo na farko tun neman mafi karancin albashi mafi yawa a Najeriya Naira 615,00 ya sauko Naira 477,000, shugabannin kwadagon sun maida wuka kube ta hanyar yin na’am da tayin da gwamnati ta yi.

Bayan kammala ganawa babban sakataren kungiyar kwadago ta TUC Komred Nuhu Toro ya ce sun amshi tayin da gabatar da hakan gaban majalisun su “mun kai majalisar kolinmu, tayin da shugaban kasa ya bayar sun kuma lamunta da shi da fatan Allah ya sa albarka…ai Naira 70,000 din nan da babu ne gara ba dadi.

Tuni ma’aikata na sassa daban-daban suka fara maida martani da mafi sauki shi ne na nuna ba abun da suka iya don jagorori sun mika wuya.

Malamin makaranta Muhammad Bello Nawaila ya ce ba wani tasiri da mafi karancin albashin zai yi in an duba dan Karen tsadar rayuwa.

Ita ma kungiyar gamayyar kungiyoyin arewa CNG da ke marawa gwagwarmayar ma’aikatan baya ta ce matukar shugaba Tinubu bai yi garambawul ga lamuran walwalar ma’aikata da matasa ba, za a iya fuskantar kalubale “mu na gujewa guguwar juyin juya hali a Najeriya matukar gwamnati ba ta farka ta dau matakan gaskiya na zahiri ba.”

Alamu na nuna batun neman karin mafi karancin albashi zai dakata zuwa wani lokaci don ‘yan kwadago sun yada gora sai komawa kan batun tsadar rayuwa.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya:

Albashi Mafi Karanci: Da Babu Gara Ba Dadi - TUCNLC.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG