ABUJA, NIGERIA - Wannan na zuwa ne bayan kammala aikin mai binciken Jim Obazee da mika rahoto a fadar Aso Rock.
Tun gabanin kammala rahoton an saki wasu bayanai na abubuwan da Obazee ya gano ciki da bankado cewa, tsohon gwamnan bankin Godwin Emefiele ya mallaki wasu bankuna da kudin almundahana baya ga kafa bankin Titan Trust.
Abun da aka kara fahimta daga rahoton shi ne zargin Emefiele da azurta wasu 'yan lele da ba su canjin dala a farashin gwamnati don cin babbar riba.
Mai taimakawa shugaba Tinubu kan labaru Abdul'aziz Abdul'aziz ya ce gwamnatin ba za ta lamunci ayyukan badakala ba. ya kuma bayyana cewa, "wannan kwamiti ya na da aiki wanda ya ke mai matukar fadi mai yawa kuma sun mika kammalellen rahoto a kan badakalar da a ka yi a babban bankin Najeriya a wadancan tsawon shekaru. Gwamnati za ta duba domin daukar mataki na gaggawa domin a tabbatar da cewa dukkanin wadanda su ka yi ba daidai ba an hukunta su kuma an kwato dukiyar jama'a da ta shiga hannun da bai kamata ba."
Lauya mai zaman kan sa a Abuja Mai Nasara Kogo Umar na daga cikin wadanda su ka bi diddigin aikin Obazee da ba da shawarar gwamnati ta aiwatar da sakamakon rahoton "hurumi na sashe na 15 sakin layi na biyar na tsarin mulkin Najeriya wanda ya dace dole ne kowane jami'in hukuma ya yaki cin hanci da rashawa da kuma amfani da kujera don gina kai. Shi Emefiele nan wurin ya yi amfani da kujerar shi ne domin ya gina kan shi."
Emefiele a na sa bangaren na musanta aikata laifi duk da ba za a iya sanin abun da ke gudana kan tuhumar a bayan fage ba.
A wani lokaci baya, mai ba wa shugaba Tinubu shawara kan siyasa Ibrahim Masari ya ce sam ba za a saurarawa Emefiele kan tuhumar gagarumar badakala ba.
Emefiele na fuskantar tuhumar a gaban babbar kotun birnin tarayya Abuja da ta Lagos.
Yanzu haka ya na hannun hukumar yaki da cin hanci EFCC a Lagos inda kotu za ta duba bukatar ba da belin sa kan tuhumar karkatar da biliyoyin dala.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:
Dandalin Mu Tattauna