Hukumar FCCPC ta ce ta fara ganin wasu bidiyo na 'yan Najeriya da ke zargin ba a barin kowa shiga shagon sai 'yan China kadai.
Shagon na hade da wurin sayar da abinci na harabar cibiyar bunkasa cinikayya ta ‘yan Sin a Abuja.
Shugaban hukumar FCCPC, Adamu Abdullahi, ya ce sun je shagon don gudanar da bincike amma sai suka tarar da shagon a rufe.
"Da muka ga haka sai muka manna takarda a kofar shagon, muna gayyatar masu shagon ofishinmu ranar Laraba don su kare kansu. Kuma hakika idan muka same su da laifi za mu rufe shagon gaba daya, saboda dokokin Najeriya ba su amince da wariya ba," a cewar Abdullahi.
Abdullahi ya kuma ce dokar hukumar ta tanadi cin tara mai yawa a kan duk wanda aka samu da laifin nuna wariya ga abokan ciniki.
Barista Yusuf Sallau Mutum Biyu, lauya ne a Abuja, ya ce yin sakaci da dokoki ke sa har wani daga ketare ya raina 'yan kasa.
Shi ma dan kasuwa, Alhaji Auwal Mbani Mbaka, ya ce a wani bangaren laifin na 'yan Najeriya ne da ke sha'awar shiga shagunan 'yan China.
Ya ba da missali da cewa a Kano saboda samun waje, akwai wani dan China da ke neman kafa kamfanin sarrafa ruwan leda, wanda ya dace a ce 'yan kasa ke irin wannan sana'a."
Yanzu dai za a jira a ga sakamakon binciken hukumar ta FCCPC game da shagon da ma matakan da zata dauka na yaki da masu sayar da kaya da tsada sosai duk da cewa dala ta sauka.
Saurari rahoton cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna