Wasu kungiyoyi biyu ne su ka rubutawa hukumar da'ar jami'an gwamnati CCB ta fito da bayanan bisa dokar 'yancin samun bayanai ta 2011.
Kin fidda bayanan ya sa kungiyoyin shigar da karar bukatar tilastawa hukumar ta saki bayanan.
Bayan rashin nasara a babbar kotun tarayya, daya daga kungiyoyin ta daukaka kara, amma nan ma kotun ta ce ba zai yiwu a saki bayanan ba, ba tare da tsari daga majalisar dokoki ba kamar yadda yake a tsarin mulki.
Kotun ta ce da karar Majalisa ya dace a shigar don tilasta ta sako tsarin don samun hurumin fidda bayanan.
Mai daukaka karar Chido Onuma ya ki amincewa da hukuncin yana mai alwashin garzayawa kotun koli.
Onuma ya zargi sashen shari'a da kawo tarnaki a samun bayanai daga gwamnati.
Dandalin Mu Tattauna