Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Shi'a Sun Yi Muzaharar Kudus A Sassan Arewacin Najeriya


'Yan Shi'a Sun Yi Muzaharar Kudus A Abuja
'Yan Shi'a Sun Yi Muzaharar Kudus A Abuja

'Yan kungiyar Shi'a almajiran Sheikh Ibrahim Elzazzaky sun gudanar da zanga-zangar marawa Falasdinawa baya kan yakin Gaza a sassa daban-daban na arewacin Najeriya.

ABUJA, NAJERIYA - Zanga-zangar mai taken ranar KUDUS ta gamu da fushin jami'an tsaro musamman a Abuja da Kaduna.

'Yan Shi'a maza da mata rike da kwalaye na adawa da matakan Isra'ila kan Gaza sun yi maci kan tituna da gefen babban masallacin Abuja su na nuna bukatar dakatar da yaki a Gaza.

A Katsina jagoran Harkar Musulunci wato IMN, Sheikh Yakubu Yahaya, ya ce iya matakin muzahar za su iya dauka don mara baya ga Falasdinawan.

A tarihi dai shi kansa shugaban na IMN, Sheikh Ibrahim Elzazzaky ya bullo da ranar ta KUDUS a Najeriya don nuna goyon bayan 'yan Shi'a masu mubaya'a ga Iran ga Falasdinawan da su ke ganin Isra'ila na tauye musu hakki.

SHugaban IMN a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky
SHugaban IMN a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky

Ya ce "ga dukkan alamu mu a nan kasar mutane su ka rika dauka tamkar al'amarin Kudus wani abu ne da ya shafi Larabawa ko ya shafi al'ummar musulmi ko ya shafi kasashe biyu Falasdinu da Isra'il, amma al'amarin ya wuce hakanan, al'amari da ya shafi bil'adama da duk mai mutunci da son gaskiya da amana. "

'Yan Shi'a Sun Yi Muzaharar Kudus A Abuja
'Yan Shi'a Sun Yi Muzaharar Kudus A Abuja
Jami'an tsaro yayin da 'yan Shi'a ke yin Muzaharar Kudus A Abuja
Jami'an tsaro yayin da 'yan Shi'a ke yin Muzaharar Kudus A Abuja
'Yan Shi'a Sun Yi Muzaharar Kudus A Abuja
'Yan Shi'a Sun Yi Muzaharar Kudus A Abuja

Mai Bishara a Kaduna Pastor Yohanna YD Buru na daga masu marawa tarukan KUDUS baya, inda ya ce "maganar Kudus ba karamin waje ba ne ga addinai guda uku, na farko addinin Yahudu, addinin Kirista da kuma addinin Musulunci. In kuma an koma ga addinin Musulunci in an bi diddigin abun sosai to 'yan Shi'a sun fi daukar zurfin maganar Kudus sosai kamar yanda Yahudawa ke dauka, shi ya sa zafin ya kai ga wannan matsayin. "

Akalla dai an jefa hayaki mai sa kwalla ga masu muzaharar a Kaduna da a Abuja.

A zamanin Shugaba Muhammadu Buhari ne gwamnatin Najeriya ta haramta aiyukan na IMN a kasar.

Ba mamaki dawo daga jinya da Sheikh Elzazzaky ya yi kwanan nan daga Iran ya zaburar da 'yan IMN kan aiyukan muzahara.

Ba kamar yanda a baya 'yan IMN kan la'anci tsohon Shugaba Buhari a muzahara ba, wannan karo ba su ce uffan kan Shugaba Tinubu ba duk da sun dora alhakin matsin tattalin arziki a Najeriya kan bin ka'idojin bankin duniya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG