Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Farashin Kujerar Hajji A Najeriya Ya Kai Naira Miliyan 8.254 Zuwa Naira Miliyan 8.464


Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON
Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON

Bisa yanda canjin dala ke hawa da sauka,  hukumar alhazan Najeriya ta ce duk wanda zai biya kujera yanzu zai bada daga Naira 8, 254, 464 a arewa sai Naira miliyan 8, 454, 464 a kudu.

Hakanan hukumar za ta rufe karbar kudi ranar Alhamis 28 ga watan nan na Maris.

Hukumar alhazan ta ce wannan bai shafi mutum 50,000 da su ka riga su ka biya kudin kujerar Naira miliyan 4.9 kafin wannan kari ba amma su ma duk da samun tallafin gwamnati za su cikato Naira miliyan 1.9.

Hajj
Hajj

Fatima Sanda Usara, mataimakiyar daraktan labaru na hukumar, ta ce, "Mutum 50,000 da tuni su ka biya kudin kujera za su yi ciko ne don sun samu tallafin gwamnati da rage-rage da hukumar ta samar. Zuwa Alhamis din nan da karfe 12 na dare za mu rufe karbar dukkan kudi don gargadin da hukumomin Saudiyya su ka yi ma na kan jinkirin."


A nan hukumar ta ce duk wanda ke son amsar kudin sa zai iya rubutawa hukumar sa ta jihar su don a biya shi.

Hajj
Hajj

Majalisar koli ta shari'ar musulunci ta bukaci gwamnatin tarayya da gwamnoni su tallafa wajen yi wa maniyyata cikaton kudin.


Malam Nafi'u Baba Ahmed shi ne babban sakataren majalisar "Zai yi wuya a iya gudanar da akin hajjin ba tare da tallafin gwamnati ba. Mu na ba da shawarar gwamnatoci su tallafa wa maniyyatan a aikin hajjin bana in ya so badi in Allah ya kai mu sai a sake sabon lale. "

HAJJ HOUSE
HAJJ HOUSE

Alkaluman hukumar sun nuna zuwa yanzu jihar Kaduna ke da mafi yawan maniyyata 4, 656 yayin da Kogi da Ebonyi ke da mafi karanci na mutum 13 kowacce, inda kuma Abia, Akwa Ibom, Anambra da Kuros Ribas ba su da ko mutum daya.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG