Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da kisan mutane biyar tare da kona kayan abinci da abubuwan hawa, a wani hari da 'yan bindiga suka kai da safiyar Litinin a garin Gidan Buwai da ke karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto da ke Arewa maso yammacin Najeriya.
Hatsabibin dan bindigar nan da ake kira Dogo Gide ya sha da kyar bayan da sojojin Najeriya suka samu nasarar hallaka wasu manyan 'yan bindiga uku a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Wani batu da ya ja hankalin 'yan Najeriya a kwanannan shi ne na wata daliba da aka kora daga makarantar nazarin kimiyar ayukkan jinya da ungozoma ta jihar Kebbi, da sunan cewa tana badala a dandalin sada zumunta na yanar gizo na Tiktok.
A Najeriya yayin da mahukunta ke kokarin lalubo mafita ga matsalar tsaro, su kuwa 'yan bindiga sai ci gaba suke yi da addabar jama'a ta hanyar kisa da yin garkuwa da su.
Alamu na nuna cewa watakila za a samu saukin matsalar rashin tsaro dake addabar wasu yankuna na Arewacin Najeriya saboda wasu gwamnoni sun fara nuna da gaske su ke yi.
Wata arangama tsakanin 'yan bindiga da 'yan banga a garin Goronyo na jihar Sakkwato ta yi sanadiyyar kashe 'yan banga hudu, da 'yan bindiga da ba'a san adadinsu ba, baya ga wani hari a yankin Wurno da ya yi sanadin mutuwar mutum hudu.
Kotun sauraren kararrakin zaben gwamna da ke zaman ta a jihar Kebbi ta yi watsi da karar da jam'iyar PDP da ‘dan takarar ta Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya suka shigar kan zaben gwaman Nasir Idris Kauran Gwandu na Jam'iyar APC da mataimakinsa Umar Abubakar Tafidan Argungu.
Har yanzu 'yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare ga al'ummomi a Arewacin Najeriya, kamar yadda yake gudana a jihar Sakkwato da ke Arewa maso yammacin kasar.
Mako guda bayan da 'yan bindinga suka sace daliban jami'ar gwamanatin tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara, a cikin daren ranar Litinin wasu 'yan bindiga sun kutsa jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto suna harbe-harbe, inda suka yi awon gaba da kayan abinci da wasu kayayyakin amfani.
Bayanai na nuni da cewa ma'aikatan ceto na can suna kokarin neman gawarwakin wadanda suka nutse a ruwan don a yi musu jana'iza.
Wasu 'yan bindiga sun sha da kyar, a lokacin da suke kokarin cin zarafin jama'a a wasu yankunan jihar Kebbi da ke Arewa maso yammacin Najeriya.
Yayin da'yan Najeriya ke dakon soma jin sakamakon kararrakin zabukan gwamnoni dake gaban kotunan sauraren kararrakin zabe, babbar jam'iyar adawa ta PDP ta fara samun galaba.
An samu tashin gobara a tashar tattara wutar lantarki ta birnin Kebbi a jihar Kebbi dake Arewa maso yammacin Najeriya a daidai lokacin da ake fama da zama cikin duhu sanadiyar katsewar na'urorin samar da wuta a sassan kasar.
'Yan Najeriya na ci gaba da kokowa akan rashin cika alkawuran da gwamnatocin suka yi musu a lokutan yekuwar neman zabuka na samar da tsaro a yankunan da ke fama da matsalar rashin tsaron.
Ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya ya yi sanadin mutuwar mutane hudu tare da ruguza gidaje masu yawa, a jihar Kebbi da ke Arewa maso yammacin Najeriya.
An kama mutane 23 da ake tuhuma da aikata ayyukan zamba da yaudara ta amfani da hanyar sadarwa ta intanet, a arewacin Najeriya, wanda hakan ke nuna yadda wannan dabi’ar ke ci gaba da yaduwa a sassan kasar.
Rundunar Sojin Najeriya ta yi wa dakarunta kashedi dangane da takon-saka da ke wanzuwa tsakanin gwamnatin Sojin Jamhuriyar Nijar da kungiyar ECOWAS.
Hakan dai na faruwa ne sakamakon takunkumi da ECOWAS ta kakabawa Nijar saboda juyin mulki da soji suka yi a kasar.
Babban hafsan Mayakan kasa Lt. Gen. Taoreed Lagbaja da babban hafsan hafsoshin kasar Lt. Gen. Christopher Musa ne suka tabbatar da hakan a Sakkwato lokacin da suka rako tsohon Babban hafsan mayakan kasa Lt. Gen. Faruk Yahaya jihar sa ta haihuwa bayan ajiye aiki.
Domin Kari