SOKOTO, NIGERIA - Wannan lamarin ya jefa tashin hankali cikin zukatan mazauna unguwanni dake makwabtaka ta tashar wutar lantarkin bayan jin karar fashewar wasu abubuwa da basu saba jin irinsa ba.
Tashar ta kamfanin dakon wutar lantarki na Najeriya da ke garin birnin Kebbi da ke tura wuta a jihohin Sakkwato, Kebbi, Zamfara da Jamhuriyar Nijar ta kama da wuta ne ranar Alhamis da dare da misalin karfe 11 da minti 30, lokacin da 'yan Najeriya ke fatar dawowar wutar lantarki da ta yi batan dabo, bayan katsewar na'urorin samar da wutar.
Faruwar wannan lamarin dai ya jefa rayukan jama'a musamman mazauna yankin da tashar wutar take cikin rudu da tashin hankali, kamar yadda wasu suka bayyana.
Wannan lamarin dai ya kara dakile fata wadda 'yan Najeriya suke da ita da samun dawowar wutar lantarki wadda tuni ake fama da rashinta tun kafin katsewar na'urorin wutar na kasa.
Kawo lokacin hada wannan rahoto dai mahukunta basu ce ko mai ba akan wannan lamarin, sai dai mutanen da wannan lamarin ya shafa sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kawo musu dauki.
Yanzu dai jama'ar jihohin Sakkwato, Kebbi, Zamfara da ma Jamhuriyar Nijar duk da yake Najeriya ta janye basu wuta, akwai yuwuwar zasu dauki wani lokaci kafin su samu dawowar wutar.
Saurari ciakken rahoton Muhammad Nasir:
Dandalin Mu Tattauna