Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Na Ci Gaba Da Kai Hare-hare A Yankunan Jihar Sakkwato


Yan bindiga a jihar Sokoto
Yan bindiga a jihar Sokoto

Har yanzu 'yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare ga al'ummomi a Arewacin Najeriya, kamar yadda yake gudana a jihar Sakkwato da ke Arewa maso yammacin kasar.

SOKOTO, NIGERIA - Al'ummomi a wasu sassan jihar Sakkwato musamman a yankin gabas na ci gaba da kokawa kan yadda suka ce har yanzu sun kasa samun yadda za su yi bacci da ido biyu a rufe saboda rashin tabbas na tsira daga hare-haren 'yan bindiga.

Ko a cikin daren ranar Laraba an sami rahoton kai hari a wani gari da ake kira Kyalkyali a karamar hukumar Sabon Birni, kamar yadda wani mazaunin garin da baya so a ambaci sunansa saboda dalilin tsaro ya sheda mana.

Haka kuma 'yan bindiga sun kai hare-hare a wasu garuruwan karamar hukumar Wurno kamar yadda shugaban karamar hukumar shi ma ya bayyana. A karamar hukumar Binji ma kusan mako daya yanzu ana samun tashe-tashen hankula sanadiyar wani harin ta'addaci da ya rikide ya koma na kabilanci. A makon da ya gabata kuma rundunar 'yan sanda ta tabbatar da samun yamutsi har da kone-kone tsakanin al'ummomi a yankin na Binji.

Wannan lamarin ba ya rasa nasaba da yadda wasu matasa suka harzuka har suka yi zanga-zangar lumana don nuna damuwa da yadda lamarin tsaro ke kara tabarbarewa a jihar Sakkwato da ma Arewa bakin daya.

Mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Sakkwato akan tsaro Kanal Ahmad A. Usman mai ritaya, ya ce gwamnati na sane da halin da jama'a ke ciki.

Masana lamurran tsaro dai sun jima suna ba da shawarwari da suke gani za su iya kawo karshen wadannan matsaloli kamar samar da rundunar tsaro ta cikin daji, da Awwal Bala Durumin Iya ke cewa, da kuma samar da cibiyar tattara bayanai tsaro na sirri da makamantansu. To sai dai aiwatar da shawarwarin watakila kan iya nuna tasirin su ko akasin haka.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG