Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kebbi: Sama Da Mutum 30 Sun Nutse A Hatsarin Kwale-Kwale


Hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi
Hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi

Bayanai na nuni da cewa ma'aikatan ceto na can suna kokarin neman gawarwakin wadanda suka nutse a ruwan don a yi musu jana'iza.

Kwale-kwalen ya dauko mutane da aka kiyasta yawan su ya wuce mutum 50, mutanen sun fito ne daga jihar Neja zuwa cin kasuwa a garin Yauri na jihar Kebbi.

Wadanda suka ga yadda lamarin ya auko sun ce iska ne mai tsananin gaske ya taso, sai taguwar ruwa ta ja kwalekwalen daga nan sai ya nutse da mutane.

Shugaban karamar hukumar Yauri ta Jihar Kebbi Bala Muhammad Yauri yace kwale-kwalen ya dauko mutane da mutane da abinci kafin lamarin ya faru.

Hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi
Hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi

Ya ce yanzu haka an samar da masu ninkaya cikin ruwa domin a gano inda kwalekwalen yake ko za'a iya gano mutanen da ya nutse da su domin a yi musu jana'iza.

Lamarin dai ya faru a jihar Sokoto mai makwabtaka da jihar Kebbi ne inda kwalekwale dauke da 'yan mata su goma sha daya ya nutse, a yankin karamar hukumar Yabo, kamar yadda dan majalisar jiha mai wakiltar yankin Abubakar Shehu Shamaki Yabo ya tabbatar.

Hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi
Hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi

Hadurran kwale-kwale sun jima suna lakume rayukan jama'a duk da kalaman da mahukunta ke yi na daukar matakan kariya daga matsalolin.

A shekakar 2021 a garin Wara mai makwabtaka da Yauri ta jihar Kebbi mutum fiye da 100 sun rasa rayukansu, bayan da wasu hadurra makamantansa da suka yi ta faruwa a wasu sassan Najeriya.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG